✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ayyana dokar ta-baci ba za ta magance matsalar tsaro ba — Masari

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya ba shawarar cewa ayyana dokar ta-baci ba za ta kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta a…

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya ba shawarar cewa ayyana dokar ta-baci ba za ta kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar ba.

Masari ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis yayin amsa tambayoyin manema labarai a Fadar Gwamnatin Najeriya bayan ganawarsa da Shugaban Ma’aikatan Fadar, Farfesa Ibrahim Gambari a Abuja, babban birnin kasar.

A Talatar da ta gabata ce, Majalisar Wakilai ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana dokar ta-baci a bangaren tsaron kasar da zummar magance kalubalen tsaro da ya dabaibaye kasar a halin yanzu.

Sai dai a cewar Gwamna Masari, babu wadatar dakarun soji da za a yi amfani da su wajen ayyana dokar ta-baci a kasar saboda ayyukan da ke gabansu a halin yanzu sun sha musu kai.

A dalilin haka ne gwamnan yake kira ga ’yan Najeriya da su daina siyasantar da lamarin tsaron kasar, inda ya ce samar da tsaro a kasar a wannan mawuyacin hali nauyi ne da rataya a wuyan kowa.

Ya ce kada a bari Najeriya ta wargaje domin kuwa hakan zai bude kofar babbar matsala a gaba daya nahiyar Afirka.

Dangane da fargabarsa a kan cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta iya biyan jihohi kasafin kudinsu na watan Mayu ba, Masari ya nemi masu ruwa da tsaki kan lamarin da su yi duk wata mai yiwuwa wajen ganin hakan ba ta faru ba.

A cewarsa, matukar jihohi da kananan hukumomi za su tsinci kansu cikin rashin samun kasafin kudin wata daga gwamnatin tarayya, hakan na iya kara rura wutar matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar.