✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ayyukan ta’addanci ba za su kare a nan kusa ba – Gwamnan Zamfara

Gwamnan ya ce matsalar ta ki karewa ne saboda akwai masu siyasantar da ita.

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya ce ayyukan ’yan bindiga da a yanzu ya rikide ya koma ta’addanci ba zai kare da wuri ba saboda mutanen da ke da hannu a cikinsa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, jim kadan bayan kammala tattaunawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Litinin.

Sai dai ya ce duk da zagon kasan da wasu ke ta kokarin yi, an samu ci gaba sosai a harkar tsaro.

Hakan a cewarsa, na da nasaba da irin jajircewar da Shugaban ke nunawa waje kawo karshen matsalar.

Gwamna Matawalle ya kuma musanta labarin da ake yadawa cewa mutum 200 ne ’yan bindiga suka kashe a garuruwan Bukkuyum da Anka na Jihar, inda ya ce hakikanin adadin mutanen 58 ne.

Da aka tambaye shi hanyar da yake ganin za a iya kawo karshe matsalar tsaro a Jiharsa, Gwamna Matawalle ya ce, “Lokacin da na fara aiki a matsayin Gwamna, na yi amfani da dabaru da dama wajen tattaunawa tsakanin makiyaya da manoma.

“A sakamakon haka, an shafe kusan wata tara babu tashin hankali, matakin ya yi tasiri sosai.

“Amma abin takaici, mutane sun yi amfani da siyasa inda suka koma wajen ’yan bindigar suka ce musu ba da gaske muke ba, ko sisi wai ba mu ba su ba.

“Hakan ya sa suka koma ayyukan ta’addancinsu, dalilin kenan da ya sa na tsame hannuna daga tattaunawar. Amma kafin nan, matakin ya yi tasiri.

“Matsala ce da na gada tun daga gwamnatocin baya, kusan shekara takwas kenan ana fama da ita, shi ya sa ba zai yiwu mu kawo karshenta a shekara biyun gwamnatina ba,” inji Gwamna Matawalle.

Ya kuma ce gwamnatinsa na zuzzurfan bincike don gano masu hannu wajen yin aiki da ’yan bindigar domin a hukunta su.