Daily Trust Aminiya - Ba a ba ni zabin gina min gida na ce a yi mana burtsatse ba
Subscribe

A hagu, Mista Pagis ne da Malam Musa da sauran manyan baqi, a yayin bikin buxe famfon burtsatse da ya gina a qauyensu

Ba a ba ni zabin gina min gida na ce a yi mana burtsatse ba – Musa Maigadi

A kwanakin nan sunan Malam Musa Usman Maigadi, dan asalin kauyen Gyallijammi da ke Karamar Hukumar Birniwa a Jihar Jigawa ya mamaye kafafen watsa labarai musamman na sadarwar zamani inda aka ce ya ki tayin yi gina masa gida ya zabi a yi wa kauyensu rijiyar burtsatse a matsayin godiya gare shi bayan ya bar aiki da wani Ba’indiye da yake yi wa gadi a Legas ba.                                                                                                                                                 To sai dai da Aminiya ta iske shi a kauyen nasu ya ce babu gaskiya a labarin da ake yadawa inda ya ce shi dai ya ja hankalin ubangidan nasa  Ba’indiye ne kan ya gina musu famfon burtsatse da zai taimaka wa al’ummar kauyen samun ruwa mai tsabta, saboda suna fuskantar matsalar ruwa sosai kuma Gwamnatin Jihar Jigawa ba ta yi masu komai ba a wannan fuska.

A tattaunawar Aminiya da Musa Maigadi, ya ce ubangidansa bai ba shi zabi  cewa ya gina masa gida ko kuma ya gina wa kauyensu wannan rijiya ba. Ya ce wannan magana kirkirarta aka yi, ba a yi wani batu mai kama da haka ba. Ya ce ubangidan nasa ne ya ji irin halin da suke ciki ya tausaya musu saboda zaman lafiyar da suke da shi.

Ya ce saboda wannan mutunci da ke tsakaninsa da mai gidansa, ne sai ya kai ziyara kauyensu kuma ya gina famfon a matsayin  gudunmawa. Haka kuma ya musanta cewa ya yi ritaya daga aiki da ubangidan nasa, ya ce har yanzu shi ma’aikacinsa ne, yana tare da shi.

Kan yadda suka hadu da Ba’indiye, sai ya ce “Ina zuwa ci-rani Legas sama da shekara 36 da suka gabata, tun ina saurayi, shi ne na gamu da mai gidan nawa, mutumin kasar Indiya, mai suna Mista Pagis. Yanzu daga haduwa da shi tsawon shekara 25 ke nan ina tare da shi a can Legas. Ina yi masa aikin gadi ne kuma duk tsawon shekara 25 din nan muna tare ba mu taba samun sabani da shi ba, kuma bai taba tafiya kasarsu ya dawo ya ga wani abu ya canja ba a gare ni. Haka kuma ni ba na sakaci da aikina. Ba na wasa da aikina, domin akwai amana tsakanina da Mista Pagis.”

Musa Maigadi ya ce lokacin da ya fara zuwa Legas, a shekarar ce aka kashe Shugaban Kasa Murtala Muhammad. “Na fara zama da shi ne a Unguwar 1004, amma yanzu ya koma Unguwar Lekki tare da ni a matsayin mai yi masa gadi,” inji shi.

Ya ce ubangidansa Mista Pagis mai yawan tafiye-tafiye ne saboda yana da kanfanin harhada magunguna kuma shi mutum ne mara kyashi, ba ya da hassada. “Kamfaninsa ne yake harhada maganin karin jini na Jabaron kuma duk lokacin da ya je unguwa ya dawo, hon daya yake yi, ba ya karawa komai dare zan tashi in bude masa kofa. Na san karar hon din motarsa saboda na saba,” inji shi.

Ya ce “A zamana da shi yau shekara 25, ban taba samun wata matsala da shi ba, a gidansa ban taba samun wata damuwa ba da shi ko iyalansa. Bai taba zuwa bai same ni ba, kullum ina bakin aikina. Ba na zuwa yawo saboda amincewarsa da ni yanzu haka da na taho gida don in dan huta yarona ne yake zaune a can a matsayin yana kula da aikin da nake yi masa.”

Kan ba ya ganin yaron nasa dan zamani ne za su iya samun matsala da shi, sai ya ce, “Babu wata matsala da zai samu saboda yana zuwa can lokaci-lokaci kuma ba wannan ne karo na farko ba da ya fara rike min aiki na taho gida. Da ma yana rike min kuma ba a taba samun wata matsala ba, don haka yanzu ma cikin amincin Allah ba za a samu ba.”

Da wakilinmu ya shaida masa cewa labari ya bazu cewa Mista Pagis ya ce zai gina masa gida a duk inda yake so saboda yana son ya faranta masa rai, ganin dadewar da suka yi a matsayin sallamarsa ta aiki, amma sai ya zabi a gina burtsatsen, sai Musa Maigadi ya  ce: “Wannan labari da ake bazawa ba gaskiya ba ne. Bai bukaci haka ba kuma bai sallame ni ba kuma ni ma’aikacinsa ne har gobe, ban ajiye aiki da shi ba. Wannan surutun mutane ne marar makama, ba ya da tushe.

 Malam Musa Maigadi da Ubangidansa Misa Pagis

Ya ce “Abin da ya faru shi ne, ya ce mini Musa, ina son in je garinku in gano kauyenku. Ni kuma na ce masa ka san ni Bafillace ne mazaunin ruga, ba a cikin gari muke ba a daji nake, wurinmu akwai iska mai zafi da kura saboda muna kusa da sahara, yana da wahalar zama. Ya ce duk da haka yana son zuwa. Shi ne ya sa rana muka hawo jirgi daga Legas muka sauka a Kano. Daga Kano muka hau motoci muka zo rigarmu.”

Ya ci gaba da cewa “Shi ne ya ga inda muke zaune kuma ya ga halin da muke ciki, ni da iyayena da ’yan uwana Fulani masu shanu. Ya ga irin wahalar da muke sha, mu da dabbobinmu a kan ruwan sha, sai mun yi tafiyar awa daya da rabi kafin mu je wurin da rijiya take kuma ita ma wajen gaba 30 kafin a jawo ruwa. Shi ne ya tausaya mana ya gina mana wannan famfon burtsatse a matsayin tasa gudunmawar. Amma kowa ya ce maka Mista Pagis ya gina mini wannan famfo a matsayin sallamata ko ya gina mini a matsayin gidan da ya ce wai zai gina min ba gaskiya ba ce, ba mu taba yin waccan magana da shi ba.”

Da Aminiya ta tambaye shi to yaya alakar kauyensu da Gwamnatin Jihar Jigawa, ko karamar hukuma? Sai ya ce, “Ba su taba yi mana komai ba, mun jima a cikin kangin rashin ruwa. Ba domin wannan mai gidan nawa ba da ya ceto mu, da ba mu san lokacin da za mu rabu da wannan kangi na karancin ruwan sha ba. Amma yanzu haka sama da garken shanu 50 ne ke samun ruwan sha a nan kuma akwai gidajen Fulani da yawan su ya kai 50, a nan suke daukar ruwa.

“Wannan famfo ya gina shi a matsayin gudunmawarsa ga ni kaina da ’yan uwana Fulani da muke fama da matsalar karancin ruwa saboda a baya muna yin tafiyar awa daya da rabi mu je mu dawo zuwa wani kauye Billagidi, nan Arewa da mu. A jakuna wani lokaci ma daga yin Asuba muke tafiya mu yi Sallah a can domin mu debo ruwa. Amma yanzu Allah Ya taimake mu wahala ta kare,” inji shi.

Kasancewar an shawo kan matsalar ruwa a kuyane yanzu wace matsala ta fi damunsu? Tambayar da Aminiya ta yi wa Musa Maigadi ke nan, inda shi kuma ya amsa da cewa “Matsalarmu rashin hanya da rashin makarantun ’ya’yan Fulani saboda mu duk abin da ake yi na bai wa Fulani makiyaya ilimi, har yanzu bai kawo gare mu ba. Ba komai ne ya sa muke cikin duhu da rashin ci gaba ba kamar rashin hanyar mota. Da a ce wutar lantarki da hanya sun zo wajenmu da rayuwarmu za ta sauya kuma da mun amfana da ilimin ’ya’ya makiyaya da Gwamnayin Tarayya take yi a ko’ina amma yanzu ba mu da ilimi ’ya’yanmu babu na boko, ba na addini; yaushe ne rayuwa za ta inganta?”

“Ba a yin maganar waya a wajenmu saboda ko garin dagacinmu in za a yi waya da wani sai da tsakiyar dare,  lokacin duniya ta yi sanyi sabis na waya yake ketarowa, muke samun damar yin waya da ’yan uwa amma wanda yake wannan yanki namu yanayin wata irin rayuwa ce marar dadi saboda muna fama da karancin abinci saboda kasarmu ta noma ta mutu, ba ta da karfi, ba ma samun takin zamani. Ko mun yi noman ba ya yin karfi zaboda rashin karfin kasa,” inji shi.

Ko yaushe Malam Musa zai dawo gida ya tsugunna domin gina kauyensu? “Ai ni har yanzu ban yanke shawarar daina zuwa Legas ba, saboda duk lokacin da na dawo gida ina yin noma, ba na wuce wata uku a nan nake komawa can saboda rayuwar can ta fi dadi a wajena. Dole in koma saboda a can ne muke samun abin da za mu ci mu sha mu taimaki ’yan uwannmu,” inji shi.

Kan sako ko kiran da yake da shi ga hukuma? Sai ya ce, “Ina son Gwamnatin Jigawa da Gwamnatin Tarayya da ma Karamar Hukumata ta Birniwa su yi koyi da wannan abin kirki na mai gidana da ya yi mana, na samar da ruwan sha a garinmu; su taimaka wajen samar da ruwan sha a yankunan karkara, musamman rugagen Fulani makiyaya irinmu. Haka ina son kamfanonin wayar sadarwa su bude rassansu, ma’ana su kafa turakunsu a nan yankin saboda ba ma iya yin waya ko za mu yi waya sai da tsakar dare kuma ba a iya samunmu sai da tsakar dare. Idan suka taimaka suka kafa mana za a samu karuwar masu hada-hada da wayar hannu da bunkasar kasuwarsu.

More Stories