✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba a bai wa bakar fata muhimmancin da ya dace —WHO

WHO ta ce kasashen duniya ba sa ba da muhimmanci ga bukatun gaggawa da suka shafi bakaken fata.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kasashen duniya ba sa ba da muhimmanci ga bukatun gaggawa da suka shafi bakaken fata a sauran nahiyoyi kamar yadda suke ba wa Ukraine.

Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, kaso kalilan daga cikin taimakon da ake ba wa Ukraine ne aka kai sauran wurare musamman a yankin Afirka da Asia.

Dokta Adhanom ya soki yadda al’ummar duniya suka mayar da hankali kan yakin da ake yi a Ukraine, yana mai cewa rikice-rikicen da ke faruwa a sauran wurare ciki har da kasarsa ta Habasha, ba sa samun kulawa kwatancin ta Ukraine, “watakila ko saboda mutanen da abin ya shafa ba fararen ba ne.”

Ya jefa ayar tambaya kan cewa shin al’ummar duniya suna bayar da muhimmanci kwantanci guda kan abin da ya shafi fararen fata da bakaken fata, inda ya buga misali da cewa ko kadan ba a samun taimakon gaggawar da ake bukata a Habasha, Yemen, Afghanistan da kuma Syria kamar yadda ake ba wa Ukraine.

Ya ce ko da yake taimakon Ukraine na da matukar muhimmanci, amma amma bai kamata a manta da sauran kasashen da ke fama da yaki, kamar yankin Tigray na Habasha, da Yemen, da Afganistan da kuma Syria ba.

A watan da ya gabata ne Dokta Tedros ya ce babu wani wuri a duk fadin duniya da lafiyar miliyoyin mutane ke fuskantar barazana kamar a yankin Tingray na Habasha.