✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a kai wa Buhari hari a Kano ba — APC

APC ta karyata PDP kan cewar an farmaki Buhari a Kano.

Jam’iyyar APC ta karyata rade-radin da jam’iyyun adawa suka yi na cewa wasu bata-gari ne suka kai wa Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari hari yayin ziyarar da ya kai Jihar Kano ranar Litinin.

Mista Bayo Onanuga, Daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, a wata sanarwa da ya fitar a daren Litinin, ya ce sabanin rade-radin, Buhari ya samu kyakkyawar tarba a Jihar.

Onanuga ya bayyana lamarin a matsayin ‘labaran karya’ daga jam’iyyun adawa.

“Ba mu yi mamaki ba game da labarin harin da jam’iyyar PDP ke ikirarin cewar an kai wa Shugaban Tarayyar Najeriya hari yayin ziyarar shi a Jihar Kano.

“Wannan harin da ake ikirarin an kai wa Shugaba Buhari, tabbas ya faru ne kawai a tunanin Sakataren Yada Labaran PDP na Kasa.

“Ya kamata ‘yan Najeriya su yi watsi da wannan labari na bogi daga jam’iyyar da ta rasa komai.

“Shugaba Buhari ya samu kyakkyawar tarba a Jihar Kano daga mutanen kirki da gwamnatin Jihar, inda ya kaddamar da ayyuka takwas,” in ji Onanuga.

Daraktan yada labarai da wayar da kan jama’a na jam’iyyar APC, ya zayyana ayyukan da shugaban kasa ya kaddamar yayin ziyarar da ya kai Jihar Kano da suka hada da gadar sama da kasa da cibiyar kula da cutar daji da dai sauransu.

Ya kara da cewar ya kamata ‘yan Najeriya su ke watsi da labaran da PDP ta ke kawowa, duba da yadda ta so wargatsa kasar baki daya.

“Mugun tunanin PDP ne kawai zai iya kai wa shugaban Najeriya hari.

“Ba abu ne mai wuya ba PDP ta dauki nauyin mutanen da ta ke biya su shirya kai harin.

“Amma, muna da tabbacin jami’an tsaro za su iya dakile duk wani shiri da aka shirya kai wa shugaban kasa kuma duk wanda aka kama tabbas zai fuskanci hukunci.

“Muna kira ga jami’an tsaro musamman ‘yan sanda da jami’an tsaron kasar nan da su gaggauta kama sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa domin yi masa tambayoyi kan wannan hari da yake ikirarin an kai wa Buhari,” in ji Onanuga.

Wannan dai na zuwa ne bayan ziyarar kaddamar da ayyukan da gwamnatin Jihar Kano da ta tarayya suka aiwatar.

A yayin ziyarar wasu fusatattun matasa sun yi wa tawagar shugaban kasa ihu tare da jifansu.