✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a kasarmu aka kama Nnamdi Kanu ba – Kenya

Ambasadan Kenya a Najeriya ya musanta cafke Kanu a kasar.

Jakadan kasar Kenya a Najeriya, Wilfred Machage, ya musanta labarin da ake yadawa kan hannun kasarsa a cafke shugaban ’yan awaren Biyafara na IPOB, Nnamdi Kanu.

Hakan na zuwa ne bayan dan uwan Kanun, Kingsley Kalu a ranar Laraba ya yi zargin cewar an cafke dan uwan nasa ne a kasar ta Kenya.

  1. Yawan mutanen da COVID-19 ta kashe a Indiya sun haura 400,000
  2. Tallafin Mai zai iya lashe N900bn a 2022 – Minista

“Bayan Nnamdi Kanu ya ziyarci Kenya jami’an tsaro sun cafke sannan suka mika shi ga hukumomin Najeriya, su kuma suka dawo da shi,” a cewarsa.

Sai dai da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Ambasada Machage ya ce “Ina so na kalubalanci duk wanda ya ce a Kenya aka kama shi da ya gabatar da hujja.

“Su zo su fada mana yaushe, ina da kuma su waye suka kama shi,” inji jakadan.

Ya ce zargin a matsayin labarin kanzon-kurege don a fusata wasu mutane na daban.

Ya ce Kenya a matsayinta na kasa ta yi mamakin jawabin da aka fitar a jaridu cewar an cafke shi a can.

Kazalika, shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasar ta Kenya, Alexander Muteshi, shima ya musanta labarin.

Kama Nnamdi Kanun da aka yi dai ya karade kafafen watsa labarai a Najeriya, sai dai Gwamnatin Najeriya ta ja bakinta ta yi gum kan inda ta kamo shi.