✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a makara wajen sake gyara Najeriya ba —Dantata

Dantata ya ce alamu na nuna cewa ba a makara wajen sake gyara Najeriya ba.

Hamshakin dan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata, ya bayyana cewa alamu sun nuna ba a makara wajen sake gyara Najeriya ba.

Dantata ya bayyana haka ne yayin wata ziyarar ta’aziyya da Kungiyar Dattawan Arewa suka kai masa bisa rasuwar Sani Dangote da kuma Alhaji Bashir Othman Tofa, wanda ya rasu a ranar Litinin.

“Za ku yarda da ni cewa tsarin tafiyar gwamnatin nan ya gaza cimma komai, abin da muke bukata shi ne sabon tsari wanda zai rage kashe kudade,” inji Dantata.

Don haka ya bayyana cewa sai dattawan sun hada kai da wasu masu kishin kasar nan sannan su yi aiki kafada-da-kafada kafin a shawo kan matsalolin da ke addabar kasar.

Dattawan na Arewa wadanda Farfesa Ango Abdullahi ya jagoranta da wasu manyan mutane da ke Kano sun kai ziyarar ce don nuna alhininsu na rashin wasu manyan mutane da aka yi a jihar, musamman a baya-bayan nan.

Daga cikin wadanda suka kai masa ziyarar sun hada da Janar Sale Maina, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, Nastura Ashir Shariff, Dokta Sadiq Gombe, Hajiya Naja’atu Mohammed da sauransu.

Kungiyar dattawan Arewan ta kuma ziyarci Fadar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Gawuna, Alhaji  Yahya Hamma da sauransu.