✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a sako Daliban Kagara ba —Gwamnan Neja

Gwamna Bello ya ƙaryata jita-jitar da ake bazawa cewa an sako daliban.

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya musanta labaran da ake yadawa cewa an sako daliban da aka yi garkuwa da su a makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Kagara a Jihar.

Gwamnan ya yi watsi a labarin ne a jawabinsa na ranar Juma’a bayan ganawa da Sheikh Ahmad Abubakar Gumi wanda ya gana da wasu shugabannin ’yan bindiga.

A ranar Alhamis Sheikh ya gana da wasu shugabannin ’yan bindigar Jihar Neja don ganin sun sako mutanen da ke hannunsu sun kuma daina aikata ta’addanci.

Bayan dawowarsa da asubahin ranar Juma’a tita-jitar sako daliban su 27 tare da malamansu uku da ma’aikatan makatarar uku da iyalansu 12 ta karade kafafen sada zumaunta.

Sai dai gwamnan wanda ya yi jawabi bayan ganawa da malamin ya ce labarin kanzon kurege ne.

Za a sako su nan gaba kadan

Tun da farko Aminiya ta kawo muku rahoton ganawar Sheikh Ahmad Gumi mai yawon yi wa ’yan bindiga wa’azi su tuba inda ya ce nan da ’yan kwanaki za a sako daliban.

Majiyarmu ta ce malamin ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da shugabannin ’yan bindiga Fulani a Dajin Dutsen Magaji ranar Alhamis, bayan da aka sace mutanen su 42 daga makarantar a daren Laraba.

Majiyar ta ce daliban tare da wasu matafiya da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su na nan lafiya kuma an kusa sako su ga iyalansu.

Ta ce Gwamnatin Jihar Neja ta amince ta yi sulhu da ’yan bindigar kuma ta tura tawagarta don tattaunawa.

Ganawar Sheikh Gumi da masu garkuwar

Shugabannin ’yan bindigar sun kai Sheikh Gumi wani kauyen Fulani da suke zargin sojoji sun kona, suka yi masa luguden bama-bamai tare da jefa gawarwakin mutane a cikin rijiyoyi.

Don haka suka sun soki matsayin Gwamna El-Rufai na Jihar Kaduna na kin sulhu ko biyan diyya ga Fulani.

’Yan bindigar Neja sun amsa kiran Sheikh Gumi

Tun da farko wata majiya ta bayyana cewa daya daga cikin shugabannin kungiyoyin ’yan bindigar, Dogo Gide ya ce a shirye suke su sako duk mutanen da ke hannunsu da zarar an biya musu bukatunsu.

Sai dai kuma bai fayyace wa bukatun nasu ba ga malamin.

Dogo Gide ya bayyana hakan ne a ganawarsu da malamin a dajin da ke Tegina a Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Malamin ya dauki matakin ba da gudunmawa ne don kashin kansa na tattaunawa da shugabannin masu garkuwa da mutane game da muhimmancin  zaman lafiya.

A yayin da yake nasiha, Sheikh Ahmad Gumi, ya kuma bayyana musu muhimmancin zaman lafiya daga mahangar Musulunci a lokacin ganawar tasu.