✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a ware wa tashar Mambila ko sisi ba

Arewa maso Gabas ta fusata saboda rashin samun kulawar gwamnati

Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas sun koka cewa ba a ware kudi wa aikin tashar lantarki ta Mambila ba a kasafin 2020.

Sakamakon haka suka yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba wa aikin muhimmanci sosai ta kuma shawo kan duk wata matsala da ke da alaka da shi.

Taron kungiyar gwamnonin yankin na ranar Alhasmis a Yola ya koka kan da abin da suka ce bai taka kara ya karya ba da aka ware domin samar da abubuwan more rayuwa a yankin a kasafin 2021.

“Naira biliyan 45.32 kacal aka ware domin samarwa da bunkasa  abubuwan more rayuwa a Arewa maso Gabas.

“Duk da matsalolin da ke addabar yankin, kashi 0.35% na kasafin 2021 na tiriliyan N13.02 aka ba yankin; wannan rahsin adalci ne idan ana batun daidaito.

“Kungiyar ta kuma yi kira ga wakilan yankin Arewa maso Gabas a Majalisar Tarayya da su tabbata an gyara rashin daidaiton”, inji takardar bayan taron da Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamwa ya karanta.

Sun kuma yi takaicin abin da suka kira rashin ba da ayyukan gina hanyoyi da kuma rashin aiwatar da wadanda ake yi a yanzu yadda ya kamata.

Don haka suka yi kira a sake duba kwangilolin sannan a kara daura damara wurin aiwatar da ayyukan a kan kari.

Taron ya yi ittifakin inganta rayuwar al’ummar yankin ta hanyar magance gibin da ake da shi na ilimi da kuma daidaita tsarin samar da ilimi daukacin a yankin.

“Mun yi nazarin matsalar ilimi a yankin muka kuma yanke shawarar zamanantar da ilimi musamman a matakin farko a fadin yankin”, inji takardar bayan taron.

Ta ci gaba da cewa: “Mun amince mu kafa Majalisar Ilimi ta Arewa maso Gabas da kuma zartar da dokokin UBEC domin karewa da kuma tabbatar da ganin kowane yaro  ya samu ilimi a matakin farko”.

Gwamnonin da suka ce an samu saukin matsalar tsaro a yankin sun koka cewa ayyukan masu satar mutane, ‘yan bindiga, barayin shanu da Boko Haram na barazana ga cigaba yankin.

“Mun yaba da kokarin hukumomin tsaro a yankin, muna kuma kokarin karfafa samar da tsaro a cikin al’ummomi domin ba da gudunmuwa ga jami’an tsaro da ke aiki a yankin”, inji sanarwar.