✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu abin da Lalong ya kawo wa Filato sai ’yan bindiga – Wike

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga daliget din PDP a Jihar Filato

Gwamnan Jihar Ribas, kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Nyesom Wike, ya ce babu wani aikin ci gaba da Gwamnan Filato, Simon Lalong ya kawo a jiharsa, sai ’yan bindiga da kashe-kashen jama’a.

Nyesom Wike, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP (daliget) daga Jihar a birnin Jos.

A cewar shi, “A kullum zaka ji an kashe mutum 10, ko 20 ko 30 ko ma mutum 100. Wannan abin takaici ne, kuma ba abu ne da za a amince ya ci gaba da faruwa ba.”

Ya yi kira ga al’ummar Jihar da su tabbatar sun zabi jam’iyyar PDP a zaben shekara ta 2023, don ceto Jihar daga wannan halin da ta shiga.

Gwamna Wike ya shaida wa wakilan jam’iyyar ta PDP cewa yazo garin na Jos ne domin ya sanar masu aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar shugabancin Najeriya.

Ya ce shi ne ya fi cancanta ya shugabanci kasar nan domin ya sake gina abubuwan da gwamnatin APC ta lalata.

Tun da farko a nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar PDP reshen Jihar Filato, Chris Hassan, ya ce tuni dama Gwamna Wike aminin al’ummar Jihar ne.

Ya ce gwamna Wike ya taimaka wajen warware matsalar jam’iyyar PDP a Jihar Filato wadda ya kai ga nasarar da ta samu kwanakin baya na lashe zaben cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai a mazabar Jos ta Arewa da Bassa.

Ya bada tabbacin cewa wakilan jam’iyyar ta PDP na Jihar za su duba wannan kokari da Gwamna Wike ya yi.

Daga cikin wadanda suka rako tawagar ta gwamna Wike akwai tsohon gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo da tsohon Antoni Janar na Najeriya, Bello Adoke da Austin Okpara da Sanata George Sekibo da dai sauransu.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Gwamnan Jihar ta Filato, Dokta Simon Manch, ta waya kan kalaman na Wike, amma bai dauki wayar ba.

Har ila yau, ya aike da sakon kar-ta-kwana, amma babu amsa, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.