✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba abin da zan bar wa ’ya’yana gado in na mutu – Buhari

Ya ce iyaye su dage wajen koya wa 'ya'yansu tsoro Allah

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga iyaye da su dada jajircewa wajen tarbiyyantar da ’ya’yansu da cusa musu tsoron Allah, ba wai mayar da hankali kan abin da za su bar musu bayan sun mutu ba.

Ya yi kiran ne ranar Laraba lokacin da ya kai wa Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk gaisuwar Sallah a fadarsa da ke Daura a Jihar Katsina.

Ya kuma yi kira ga matasa kan su kara dagewa wajen neman ilimi ba wai aikin gwamnati ba wanda a yanzu ba ya samuwa, inda a maimakon haka ya ce kamata ya yi su fi mayar da hankali wajen koyon sana’o’in hannu domin yaki da talauci.

Ya ce kamata ya yi a fi mayar da hankali koya musu sana’o’i domin su sami kwarewa, inda ya ce, “Lokacin annobar COVID-19, mun umarci dukkan ma’aikatan da ke matakin albashi na 12 zuwa kasa su yi aiki daga gida, kuma abin mamaki babu abin da ya tsaya.

“Na sha mamakin abubuwan da na gani bayan shafe shekara uku ina jan ragamar kasar nan. A wannan gabar ce na gane haka, kuma na fada wa ’ya’yana cewa babban jarinsu shi ne ilimin da ke kansu, ba wai abin da suka mallaka ba.

“Babban abin da na fi mayar da hankali a tarbiyyantar da yara shi ne su dage su zama masu amfani a duk inda suka tsinci kansu. Na fada musu, musamman ma mata daga cikinsu cewa zan aurar da su ne kawai bayan sun kammala karatun digirinsu na farko.

“Sun riga sun sani, babu abin da zan bar wa kowa ya ci gado. Babban gadon da zan bar musu shi ne ingantaccen ilimi,” kamar yadda Buhari ya fada a cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Garba Shehu ta rawaito.

Buhari ya kuma shada wa Sarkin na Daura cewa zai rika zuwa fadar yanzu a kai a kai a shirye-shiryen mika mulki a badi, inda ya ce yanayin aiki ne ya sa ya shafe tsawon lokaci bai kai ziyarar ba.

“Wannan ne lokaci mafi tsawo da na taba shafewa ban zo Daura ba. A zahirin gaskiya ma sai da Sarki ya yi kokarin hada ni da jama’a a Filin Idi, inda ya ce na shafe kusan shekara ban zo Daura ba,” inji Buhari.

Da yake nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya jero nasarorin da ya ce gwamnatin Buhari ta samu, ciki har da a bangaren tsaro, inda ya ce a kowanne wata a kan ba su wasu kudade domin su tabbatar da shi.

Shi kuwa Sarkin na Daura jinjina wa Buhari ya yi kan manyan ayyukan raya kasar da ya kawo masarautar, inda ya ce akasarinsu har yaran da ba a haifa ba za su ci gajiyarsu.