Ba abin kunya ba ne don NECO ta biyo mu bashi —Gwamnan Neja | Aminiya

Ba abin kunya ba ne don NECO ta biyo mu bashi —Gwamnan Neja

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello
    Abubakar Akote, Minna da Sani Ibrahim Paki

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya amsa cewa Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO) na bin jiharsa bashin kudaden jarrabawa na shekarar 2021.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai yayin wata zantawarsa da su a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Minna, ranar Laraba.

Gwamnan ya ce, “Ba abin kunya ba ne. Ai bashi hanji ne, ko kai na san ana bin ka, babu wani abin kunya a ciki.

“Gaskiya ne ana bin mu bashi saboda lokacin da gwamnatin da muka gada ta fara wasu daga cikin wadannan ayyukan, tattalin arziki ba shi da wata barazana, akwai wadatattun kudade, ba irin yanzu da muke cikin masassara ba.

“Hatta tafiyar da harkokin gwamnati na yau da kullum ma yanzu nema yake ya gagara,” inji Gwamnan.

Sai dai ya ce tuni gwamnati ta biya wani kaso na kudin ga hukumar.

“Shi fa bashi hanji ne, kana cinsa ne in ka san zaka iya biya.”

Aminiya ta gano cewa dalibai daga makarantun sakandaren Gwamnatin Jihar sun sami damar ganin sakamakon jarabawarsu ta 2021 ne mako daya bayan an sake ta.

Bugu da kari, a bangaren tsaro kuwa, Gwamna Sani Bello ya tabbatar da cewa yanzu haka akwai mayakan kungiyar ISWAP da na Boko Haram a wasu sassa na Kananan Hukumonin Shiroro da Munya da kuma Rafi na Jihar.

Sai dai ya ce batun satar shanu ya ragu matuka a Jihar tun bayan da sojoji suka toshe hanyoyin da ’yan bindigar ke bi domin kai hare-hare a yankunan.