✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba da gangan na taka hoton Kwankwaso ba —Ganduje

Ganduje ya sanar da hakan ne ta hannun kwamishinan yada labaran jihar Kano.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi martini kan cece-kuce da ake yi kan taka hoton tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da ya yi.

Wasu hotuna sun bayyana a ranar Asabar inda suka nuna Gwamnan yayin karbar wasu da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar yana taka hoton, ko da yake ya ce ba da gangan ya aikata hakan ba.

  1. ’Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Filato
  2. An kashe Fulani 16,000 a bana — Miyetti Allah

Ya bayyana hakan ne ta hannun Kwamishinan Watsa Labaran Jihar, Malam Muhammad Garba a cikin wata sanarwa ranar Litinin.

Ganduje lokacin da ya taka hoton Kwankwaso

A cewar Kwamishinan, “Lokacin da Gwamna Ganduje ya taso don zuwa wajen  yin jawabi, tsofaffin mabiya Kwankwasiyya sun taso don yi masa iso.

“Wani daga cikin tsofaffin mabiya Kwankwasiyyar ne ya jefar da hoton tsohon gwamnan shi kuma mai girma Gwamna Ganduje ya bi ta kai ba tare da ya sani ba,” cewar Garba.

Aminiya ta rawaito yadda Ganduje a ranar Asabar yayin gangamin karbar wasu ’yan siyasa da suka sauya sheka zuwa APC ya taka hoton tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Tuni mutane da dama suka yi ta Allah-wadai da lamarin suna cewa hakan bai dace ba, ciki kuwa har da tsohon Kwamishinan Ayyukan Jihar, Injiniya Mu’azu Magaji.

Sai dai sanarwar da Kwamishinan Watsa Labaran ta ce duk da bambacin ra’ayin siyasa da ke tsakanin Ganduje da tsohon mai gidan nasa, ba zai taba aikata hakan don kaskantar da shi ba.

Ya kara da cewar, an yi wa lamarin mummunar fahimta ne don kara gishiri a ciwo.

Kwamishinan, ya kuma cewa kowa ya san Ganduje mutum ne mai martaba mutane da son zaman lafiya.