✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba daidai ba ne a katse hanyoyin sadarwa a Zamfara da Katsina – SERAP

SERAP ta bayyana matakin a matsayin wani yunkurin hukunta mazauna Jihohin.

Kungiyar nan mai Fafutukar Tabbatar da Adalci a Al’amuran Mulki (SERAP) ta soki lamirin Gwamnatin Tarayya kan katse hanyoyin sadarwa a Jihar Zamfara da wasu sassa na Jihar Katsina.

Kungiyar dai ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya umarci Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami da Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Kasa (NCC) da su gaggauta dawo da harkokin sadarwa a Jihohin.

A kwanan nan ne dai NCC ta umarci kamfanonin sadarwa da su datse dukkan hanyoyin sadarwar a Jihar Zamfara da kuma wasu Kananan Hukumomi guda 13 a matsayin irin matakan da ake dauka don magance matsalar ayyukan ’yan bindiga a yankin.

Sai dai SERAP a cikin wata budaddiyar wasika mai dauke da kwanan watabn 11 ga watan Satumbar 2021 mai dauke da sa hannun shugabanta, Kolawole Oluwadare ta ce matakin ba ya kan doron doka.

A cewar wasikar, “Dakatar da intanet da sauran harkokin sadarwa a Jihohin Zamfara da Katsina, ba tare da wata kwakkwarar hujja ba ya saba da hankalin duk wani mai tunani.

“Katse hanyoyin wani mataki ne na hukunta ’yan Najeriya da ke zaune a yankunan.

“Lamarin na da mummunar illa da tarnaki ga walwalar ’yan kasa, musamman in aka yi la’akari da yadda dama ’yan kasar ke ci gaba da rayuwa cikin takura, bai kamata a ce an sake kakaba musu wannan matakin ba,” inji SERAP.