✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba Dangote ne kadai ke shigo da siminti da sukari da gishiri Najeriya ba

An ba su lasisin amma ba a ba su damarmakin da Dangote yake cin moriyarsu ba.

Aminiya ta bi diddigin wani ikirari da aka yi a makonnin bayan nan da ya ce Aliko Dangote ne kadai yake da lasisin shigo da sukari da siminti kasar nan.

Zargi: Wani lauya mai yawan jawo ce-ce-ku-ce, mai suna Malcolm Omirhibo, ya yi ikirarin cewa Alhaji Aliko Dangote wanda shi ne ya kafa Rukunin Kamfanonin Dangote, cikin shekaru, ya kasance dan kasuwa guda daya tilo da aka bai wa lasisin shigo da wasu kayayyaki cikin kasar nan duk da kasancewar Najeriya tana tafiyar da tsarin kasuwanci ne marar shinge.

Hukunci: Ikirarin shafin gizo ne kawai. Kodayake, an sha zargin Dangote da zama shalelen gwamnati wanda hakan yake ba shi damar habaka harkokin kasuwancinsa; binciken wakilinmu ya gano cewa gwamnati ta ga dacewar ta rika ba da lasisi ga ’yan kasuwar da suka cancanci shigo da wasu ababuwa a fannonin arziki daban-daban, wadanda masu gogayya da Dangote suna ciki.

Cikakken bayani: Wani lauya mai yawan jawo ce-ce-ku-ce, Malcolm Omirhibo, ya wallafa a shafinsa na Twitter a cewa, attijirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya tara dukiyarsa ce ta dalilin zama dan gaban goshin gwamnati tare da zama shi kadai gwamnatin take bai wa lasisin shigowa tare da sayar da siminti da sukari da kuma gishiri.

Kamar yadda ya wallafa: “Ta yaya za a ce kasar da ke da al’umma fiye da mutum miliyan 200 kuma take ikirarin ita kasa ce ta dimokuradiyya mai tsarin kasuwanci marar shinge za ta bai wa mutum guda daya tilo lasisin shigo da sayar da siminti da sukari da kuma gishiri?

“Yanzu an kuma sake ba shi lasisi shi kadai na gina matatar mai daya tilo. Abin ba ya da wata ma’ana sam.”

Makalar da ya wallafa mutum 4,547 suka sake wallafa ta yayin da wadansu 432 suka ambace ta, sai kuma wadanda suka nuna suna son abin da ya wallafa su 10, 300 a shafin na Twitter.

Sai dai wani tsokacin da wani mai suna Babatunde Felid ya ce, “Ba gaskiya ba ne… zancen gaskiya lamarin ya danganta ne da irin dabarun iya kasuwancin wadanda yake gogayya da su… daga dan abin da na sani dukkan masu gogayya da shi a harkar siminti da sukari suna iya bakin kokarinsu.

“A takaice, cikin kwanakin nan ma na fi ganin sukarin Kamfanin Golden Penny fiye da na Kamfanin Dangote.”

Wani mutum mai amfani da sunan Misipe01 shi ma ya karyata lauyan da cewa, “Sam ba ka fadi gaskiya ba!

“Tsohuwar Hukumar Kula da Albarkatun Mai ta DPR ta ba da lasisin gina matatun mai masu yawa sai dai ’yan kasuwar sun kasa gina matatun man.

“Don Allah, nan gaba kafin ka wallafa abu ka tabbatar ka tantance hujjojinka kafin ka fito ka fada wa jama’a. Na gode.”

Lokacin da wani mai amfani da Twitter, @ElMali, ya yi tambaya cewa, “Shin su sauran mutanen sun nemi lasisin ne aka hana su?”

Sai wani mai suna @Origin1Nigerian ya mayar da martanin mara baya ga lauyan yana cewa, “An ba su lasisin amma ba a ba su damarmakin da Dangote yake cin moriyarsu ba.

“Don haka, jiya-i-yau ne kawai.”

Har wa yau, wani mai amfani da sunan @IgweFrank18 ya ce, “Haha, wasu lokutan nakan ji ina ma a ce ni dan Ghana ne, sai dai ba zan guje wa kasata abar sona ba Najeriya.

“Mun girma amma tamkar ba mu girma ba saboda shekara da shekaru maganar guda ce.

“Gare ku matasa, makomarku ta fi muhimmanci a kan abin da gwamnatin nan take muku muradinsa.

“ Ina mai shawartar matasa su kauce wa wannan hirar.”

Tushen zancen: A lokuta da dama, mashahurin attajirin Afirkar kuma kasaitaccen dan kasuwar, Aliko Dangote, an sha zarginsa da tara dukiya ta hanyar cin gajiyar manufofin gwamnati wadanda suke taimaka masa fadada harkokin kasuwancinsa, maimakon amfani da tsagwaron dabarunsa na kasuwanci.

Duk da an fi saninsa da sarrafa siminti, amma Alhaji Dangote shekaru da dama ya kasance yana zuba jari a wasu fannonin tattalin arziki na daban a cikin Najeriya.

Na baya-bayan nan shi ne kamfanin sarrafa taki da kuma matatar mai wacce za ta fara aiki a badi.

Masu sukarsa na danganta bunkasar arzikinsa da kusancin da yake shi ga masu iko, suna cewar harkokin kasuwancinsa na bunkasa ne ta dalilin kirkiro da tsarin BIP.

Mene ne BIP: Yana nufin tsarin da kamfani zai sayo ko kuma samar da wasu ababuwan da yake bukata wajen sarrafa kayayyakinsa ta yadda zai samu damar samarwa ko sarrafa wasu abubuwan da yake bukata domin aikace-aikacensa.

Hakan zai taimaka wa tattalin arziki ya bunkasa da kawo sauyi a harkar tattalin arziki tare da samar da ayyuka ta hanyar zaburar da amfani da kayayyakin da aka samar a cikin Najeriya a fannonin da suka jibanci sarrafa kayayyakin amfani.

A Najeriya, kirkiro da tsarin na BIP a harkar tattalin arziki daidai yake da kishin kasa wanda yake da zimmar bunkasa tattalin arzikin ta hanyar karfafa gwiwar sarrafawa ko samar da kayayyaki a cikin gida Najeriya ta hanyar dafa wa kamfanonin.

Gwamnati takan yi haka ne ta hanyar daga wa kamfanonin kafa daga biyan haraji dabandaban na wani lokaci da zimmar bunkasa bangaren da ake bukata ya habaka tare da tabbatar da ya tsaya da kafafunsa, yayin da sannu a hankali, a daya bangaren, ake rage shigo da kayayyakin da fannin yake sarrafawa.

Wannan yana kunsar kamfanonin ’yan kasuwa masu neman a sahale musu shigo da na’urori da injina ko kuma danyen abin da ake bukata domin sarrafa kaya, inda a daya hannun ake ba da damar shigo da ainihin kayan da aka sarrafa domin kada ya yi karanci a cikin kasa.

Kayayyaki kamar sukari da gishiri da siminti da ruwan lemo na daga cikin kayayyakin da suka amfana da tsarin, sai dai sakamakon da aka samun ya bambanta, inda na siminti ya janyo ce-ce-ku-ce sosai.

Duk da yake an samu nasarar muradin sarrafa shi a cikin kasa inda Najeriya a halin yanzu take fitar da siminti zuwa wasu kasashen Afirka, tsadar simintin a Najeriyar ta haifar da kiraye-kiraye ga gwamnati kan ta bullo da karin tsare-tsare ko manufofin da za su sa wasu kamfanonin su shigo a fafata da su, inda hakan zai sa farashin ya rikito.

Shin Najeriya tana shigo da sukari da gishiri da siminti?

Sai dai duk da tsarin na BIP ga wadannan fannonin tattalin arzikin guda uku, har yau Najeriya na shigo da wadannan kayayyaki koda dai ana sa tsauraran matakai yayin da Babban Bankin Najeriya yake da ikon fada-a-ji kan wadanda za a bai wa Dalar Amurka da ake bukata domin sayo kayayyakin.

In ban da siminti kadai, duka biyun nan kusan ana shigo da su a danyensu -duka biyu saboda tsarin na BIP ya bai wa Najeriya damar sarrafa su a cikin kasa.

Sai dai hanzari ba gudu ba, kamfanoni kalilan ne suke damawa a bangaren sarrafa sukari da gishiri sakamakon tsadar gudanar da kamfanonin ta yadda za su ci gaba da aiki a cikin kasar.

Shin Dangote ne kadai a Najeriya ke shigo da wadannan kayayyaki?

Siminti dai Dangote ba ya shigo da shi cikin kasa kamar yadda kamfaninsa yake kan gaba a sarrafa shi a Najeriya.

A nan Kamfanin Dangote yana gogayya da wasu kamfanoni guda biyu: Kamfanin Siminti na BUA da Kamfanin Siminti na Lafarge a matsayin ja-gaba a fagen sarrafa siminti a Najeriya, inda suke jan akalar kashi 80 cikin 100 a sana’anta siminti.

Batun sukari kuwa, Kamfanin Dangote yana shigowa ne da danyen sukari, inda yake sarrafa shi a cikin kasa.

Tsarin kasa na samar da sukari ya yi tanadin cewa danyen sukarin da za a shigo da shi cikin kasa ya dogara ne da yadda kamfanonin suka himmatu wajen samar da danyen sukari a cikin Najeriya (fadamun noman rake).

A nan, Kamfanin Dangote yana gogayya ne da Kamfanin Flour Mills of Nigeria da Kamfanin BUA Foods.

A kan gishiri kuwa, wasu daga cikin abubuwan da ake bukata domin sarrafa shi ana shigowa ne da su cikin kasa, sai dai kamfanin yana da wajen sarrafa shi domin aiki da shi a cikin kasa.

A nan Dangote yana gogayya ne da Kamfanin Premium Salt da Bayswater Industries Limited da suke sarrafa gishirin Mr Chef da Union Dicon Salt Limited da Columbia International Limited da Royal Salt Limited da dai makamantansu.

Karkarewa: Sakamakon binciken ya nuna cewa Dangote ba shi kadai ne ke jan zarensa a fagen shigo da wadannan abubuwan da aka zayyana ba- a yanzu ko a can baya.

Sai dai zargin cewa yana samun damarmaki na musamman daga hukumomi suna kara samun gindin zama, amma akwai hujjojin da ke nuna cewa yana da masu gogayya da shi a duk sha’anin harkokin kasuwancinsa.