✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar bai daya a Najeriya —Ma’a’ikatan Jami’a

Gamayyara kungiyoyin jami’o’i sun ce ba su da masaniyar umarnin Buhari cewa Ministan Ilimi ya sasanta da su cikin sati biyu

Gamayyar Kungiyoyin Manyan Malaman Jami’o’i (SSANU), da ta Ma`aikatan da ba Malamai ba (NASU), sun ce su ma a jarida suka karanta cewa Buhari ya ba wa Minista mako biyu ya kawo karshen yajin aikinsu.

Don haka, sun ce babu fashi a zanga-zangar bai-daya da Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta shirya jagoranta ranar Talata domin nuna fushinsu kan shakulatin bangaro da bukatun kungiyoyin da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Kakakin gwamayyar kungiyoyin kuma Sakataren NASU, Peters Adeyemi ya bayyana cewa, “Babu wata takarda a hukumance da aka ba mu da za ta nuna cewa an bai wa Ministan Ilimi wannan umarni na share mana hawaye cikin sati biyu; mu ma a jarida muka karanta kamar kowa”, in ji Adeyemi.

Ya bayya cewa don haka, babu abin da zai zai hana su fitowa kan tituna domin gudanar da zanga-zangar ta bai-daya da NLC ta kira.

Ya kuma bayyana rashin gamsuwa da rahoton Kwamitin da Farfesa Nimi Briggs ke jagoranta ya mika ga Gwamnatin Tarayya domin sanya hannu.

Gwamnatin Tarayya dai ta kafa kwamitin ne tun a watan Maris domin shiga tsakanin a zaman tattaunawar kungiyoyin da gwamnatin.

To sai dai kungiyoyin sun ce akwai son rai a lamarin kwamitin, kasancewa babu batun karin albashin mambobinsu da kaso 10 da aka amince da shi a rahoton nasu.