✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ba kisan gilla aka yi wa shugaban hukumar NECO ba’

A cewar iyalan, ya mutu ne sakamakon wata gajeriyar rashin lafiya a gidansa da ke Minna.

Sabanin rahotannin da kafofin labarai suka yi ta yadawa cewa kisan gilla aka yi wa Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO), Farfesa Godswill Obioma, iyalansa sun ce mutuwar Allah da Annabi ya yi.

A cewar iyalan, Farfesan ya mutu ne sakamakon wata gajeriyar rashin lafiya, a gidansa da ke Minna a ranar Litinin yana da shekara 67.

Daraktan kula da ma’aikata na hukumar, Alhaji Mustapha Abdul, shi ya sanar da mutuwar shugaban hukumar ranar, Talata yana mai ambato iyalan marigayin na cewa ya mutu ne sakamakon rashin lafiya.

A cewar sanarwar, “Wannan ya ci karo da yamadidin da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa kisan gilla aka yi wa shugaban hukumar a gidansa da ke Minna.

“Da wannan sanarwar muke kira ga ma’aikatan hukumar da su kwantar da hankalinsu sannan su yi wa marigayin addu’a,’’ inji shi.

An haifi Farfesa Obioma ne ranar 12 ga watan Disamban 1953 a Karamar Hukumar Bende ta Jihar Abiya.  

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi Shugabancin hukumar NECO ranar 14 ga watan Mayun bara. 

Gabanin nadin nasa, ya rike mukamai a wurare da dama, ciki har da Kwamishinan Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), a  Jihar Ebonyi.

Ya mutu ya bar mata daya da ’ya’ya.