✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba lallai Najeriya ta kai badi a matsayin kasa daya ba — Soyinka

Ko a makon da ya wuce dai sai da Soyinka ya goyi bayan masu yunkurin ballewa daga kasar.

Fitaccen marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka ya yi gargadin cewa Najeriya na dab da wargajewa kuma akwai yuwuwar abubuwa su kara tabarbarewa muddin gwamnati ta ki waiwayar bukatun ’yan kasa.

Ko a makon da ya wuce dai sai da Soyinka ya goyi bayan masu yunkurin ballewa daga kasar inda ya ce suna da ’yancin neman yin hakan.

A yayin wata tattaunawarsa da gidan Talabijin na Arise ranar Talata, Farfesan ya yi gargadin cewa tayar da kayar bayan da ake fuskanta a wasu sassa na Najeriya na iya kazancewa muddin gwamnati ta gaza yin abin da ya dace.

Da aka tambaye shi ko Najeriya za ta iya ci gaba da zama a matsayin dunkulalliyar kasa, sai ya ce, “Bana tunanin hakan in dai abubuwa za su ci gaba a haka, ko aka ki sauya fasalin gwamnati.

“Dalilin da ya sa kenan mutane suka hassala suke fantsama tituna suna zanga-zanga, duk kuwa da barazanar jami’an tsaro.

“Ba wai Soyinka ne kawai ya taba fadar haka ba. Mutane da dama sun fadi haka; tsofaffin Shugabannin Kasa, ’yan siyasa da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum da masana tattalin arziki duk sun fadi haka. Har ma mun gaji da jin hakan.

“Ina jaddada cewa wannan kasar ta dauki hanyar lalata kanta da kanta, matukar Buhari da gwamnatinsa ba su saurari jama’a da koke-kokensu ba, to ba lallai ne Najeriya ta sake yin bikin Ranar Dimokradiyya ta badi ba.

“Alal misali, ka dauki matsayin Gwamnonin Jihohin Kudancin Najeriya a kan hana kiwo, kusan rabin Gwamnonin kasa, a tsari irin na mulkin Dimokradiyya sun ce basa son abu, sannan kawai wani ya zauna ya harde kafa a Fadar Shugaban Kasa ya ce ya umarci babban lauyan gwamnati ya kafa wata doka da ta yi kama da ta Turawan Mulkin Mallaka.

“Abin da hakan ke nunawa shine ba ya sauraron jama’a, ba ya sauraron abin da gwamnatocin da ke wakiltarsu ke cewa. Na kan ji takaici a duk lokacin da na ji makamantan irin wadannan batutuwan,” inji Soyinka.