✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba lallai ne a sami Ukraine a taswirar duniya ba nan da shekara 2 — Rasha

Rasha ta ce babu tabbacin Ukraine za ta kara shekara biyu ban gaba

Tsohon Shugaban Kasar Rasha, Dmitry Medvedev, ya yi gargadin cewa ba lallai a sami kasar Ukraine ba kwata-kwata a taswirar duniya nan da wasu ’yan shekaru masu zuwa.

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da Rasha ke ci gaba da luguden wuta a kokarinta na kwace iko da manyan biranen Ukraine.

Medvedev, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Tsaron Rasha ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Telegram ranar Alhamis.

Ya ce, “Na ga sakonku cewa Ukraine na son fara karbar iskar gas daga abokan huldarta na ketare da zummar cewa za ta biya cikin shekaru biyu masu zuwa.

“Abin tambayar a nan shi ne: wa ma ya fada muku cewa nan da shekaru biyu masu zuwa za a sami Ukraine a taswirar duniya?” inji shi.

Sai dai wani hadimin Shugaban Kasar ta Ukraine, Mykhailo Podolyak, ya mayar masa da martani a shafinsa na Twitter.

“Ukraine ta wanzu, tana wanzuwa kuma za ta ci gaba da wanzuwa. Abin tambayar shi ne ina Medvedev zai kasance nan da shekara biyu?” inji Mykhailo.