✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ma goyon bayan yajin aikin masu gurasa — Masu sayarwa

Muna nan a kan bakanmu domin mai daki shi ya san inda yake masa yoyo.

Kungiyar Masu Sayar da Gurasa ta Jihar Kano ta nuna rashin goyon bayanta game da yajin aikin da  masu sana’ar gurasa suka tsunduma a ranar Litinin.

Sakataren a Unguwar Jakara, Hadiyyatullah Muhammad ya fada wa Aminiya cewa mambobin kungiyar sun ki shiga yajin aikin ne duba da rashin tuntubar su da kungiyar masu gurasar suka yi.

“A matsayinmu na masu ruwa da tsaki a wannan sana’a, ya kamata a ce an tuntube mu kafin a kai ga wannan mataki. 

“Sai ji kawai muka yi a gari an shiga yajin aikin. Babu shakka mun san fulawa ta tashi amma wannan abu ne da za a iya warware shi cikin sauki.

“Illa iyaka za a iya kara kudin gurasar ko kuma a rage zubinta. Na tabbata masu amfani da ita za su iya saye a kan hakan.”

Sai dai ya ce yajin aikin bai yi wani tasiri ba, sannan ya yi kiran da a zauna a teburin sulhu. 

“Kamar yadda kike gani gashi nan muna sayar da gurasar duk da cewar ba a samu gurasar kamar yadda aka saba ba.

“Ya kamata su zo a zauna a teburin shawara. A yi tunanin fito da hanyoyi da wannan sana’ar za ta inganta ta kuma ci gaba madadin yajin aikin da ba zai haifar wa sana’ar da mai ido ba.”

Karancin gurasar 

A ziyarar da Aminiya ta kai Unguwar Jakara inda nan ne wurin da ake hada-hadar gurasar, wakiliyarmu ta iske ana ci gaba da kasuwancin gurasar duk da yake akwai karancinta ba kamar yadda aka saba ba.

Malam Ado dogo mai nama, mai sana’ar gasa balangu ne a birnin Kano wanda kuma yake gudanar da sana’arsa kamar yadda ya saba ya ce ya sami karancin gurasa wanda ya yi fatan kawo karshen yajin aikin.

Shi ma wani mai sayar da tsire mammallakin Kamfanin Sauki Suya Spot ya bayyana rashin jin dadinsa game da yajin aikin na masu gurasar inda ya ce hakan ya janyo karancin gurasar wanda kuma ya shafi farashinta.

Yajin aikin na nan daram 

Sai dai a hirarsa da Aminiya, Sakataren Kungiyar Masu Sarrafa Gurasar na Jihar Kano, Malam Ahmad Rufa’i Tanko ya bayyana cewa suna nan a kan bakansu na yajin aikin domin mai daki shi ya san inda yake masa yoyo.

Ya kuma musanta batun da masu sayar da gurasar ke yi na cewa ba a sanar da su ba inda ya ce da farko sun zauna da su domin a samu maslaha amma hakan ya gagara.

“Mun fara zama da su yadda za a yi musu karin kudi sai dai su ba su amince da hakan ba inda suka nemi sai dai a rage girman gurasar kawai,” inji shi.

Dalilin rashin shiga yajin 

Sakatare Malam Ahmad Rufa’i Tanko ya zargi wadansu mambobin kungiyar masu sarrafa gurasar da rashin kishi da neman yi wa yajin zagon kasa.

“Kin san akwai marasa kishi a cikinmu to irinsu ne suka yi gurasar, kuma ba wadanda suka gaji sana’ar daga iyayensu ba ne. 

“Wadanda ba su san darajar sana’ar ba ne. Amma masu gurasa irin su gidansu Alhaji Mamman na ‘Yan gurasa da Gidan  Babbar Mace duk ba su yi gurasa a yau (Litinin).

“Su kuma masu sayar da gurasar, idan ma ba su shiga yajin aikin ba, ba mamaki domin su ba su da asara mu muke yin gurasa da kudinmu ko bashi. 

“Idan sun karba su sayar idan ba su sayar ba sai su dawo mana da ita.  Mu ne da asara. 

“A irin haka mambobinmu da yawa sun ci bashi har kudi sun karye musu a kai.”