✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ma karbar dauki daga makiya —Lebanon ga Isra’ila

Gwamnatin Lebanon ta mayar da tayin Isra’ila na yin magani ga wadanda suka jikkata sakamakon fashewar wasu ababe da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 100…

Gwamnatin Lebanon ta mayar da tayin Isra’ila na yin magani ga wadanda suka jikkata sakamakon fashewar wasu ababe da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 100 ta raunata 4,000.

Lamarin ya faru ne a Beirut, babban birnin kasar ta Lebanon, a ranar Talata.

Daraktan wani asibiti da ke arewacin Isra’ila ya roki shugabannin Lebanon cikin harshen Larabci da su ba su damar yi wa mutanen da suka jikkata magani.

“Mu kawai muna son bayar da agaji ne, duk wanda ya zo, za mu yi masa magani kuma ya samu sauki”, inji Dakta Masad Brahoum, shugaban Galilee Medical Center, cikin harshen Larabci a wani gidan rediyo.

Jami’an gwamnatin Lebanon da suka yi raddi ga tayin da kasar Isra’ila ta yi na turo jami’an lafiyarta ta kafar da ta dace a daren Talatar sun ce “Ba ma karbar taimako daga makiya”.

Makwabtan biyu na zaman doya da manja kuma babu huldar diflomasiyya a tsakaninsu.

Har yanzu dai ba a kai ga bayyana musabbabin fashewar ababen da suka jikkata mutanen ba.

Lamarin ya sa kashen duniya irinsu Amurka da Iran da Faransa da Jamhuriyar Czech suka tausaya tare da yin tayin kawo dauki domin a shawo kan lamarin.

Shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Lebanon, Abbas Ibrahim,
ya danganta lamarin da wani makamashin ammonium nitrate da gwamnatin kasar ta kwace daga wani jirgin ruwa a gabar takun kasar, a shekarun da suka gabata.