✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu fatan sake samun yakin basasa a Najeriya —El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce Najeriya ba ta fatan sake samun yakin basasa kamar yadda ya auku a 1967. El-Rufai ya fadi haka…

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce Najeriya ba ta fatan sake samun yakin basasa kamar yadda ya auku a 1967.

El-Rufai ya fadi haka ne a lokacin da yake yi wa masu yi wa kasa hididima da aka tura jihar jawabi a yayin kammala zamansu a sansanin horarwa ranar Talata a Kaduna.

Ya ce zai kyautu matasan Najeriya su nesanta kansu daga dukkan abun da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar kasar nan.

Daga nan, ya gargadi ’yan hidimar kasar da za a yi amfani da su wajen gudanar da zaben 2023 da kada su bari a yi amfani da su wajen tafka magudi.

Da yake jawabin ta bakin mukaddashinsa, Hadiza Balarabe, El-Rufai ya ce yakin basasa al’amari ne wanda Najeriya ba ta fatan sake ganin irinsa.

“Dole ne matasa su tuna cewa an assasa NYSC ne bayan yakin basasan da ya yi wa kasa illa.

“Yaki ne wanda babu bukatarsa, wanda kuma ba mu fatan ya maimaita kansa.

“Don haka, wajibi ne matasan Najeriya su nesanta kansu da duk wani abu da ka iya haifar da tashin-tahina a kasa.

“A matsayinmu na kasa, dole mu kiyaye sake aukuwar duk wani mummunan lamari da ya taba faruwa ga kasa,” in ji gwamnan.