Ba mu hana yin tashe a Kano ba —’Yan sanda | Aminiya

Ba mu hana yin tashe a Kano ba —’Yan sanda

Wasu yara suna tashe. (Hoto: DW).
Wasu yara suna tashe. (Hoto: DW).
    Sagir Kano Saleh

’Yan sanda sun bayyana cewa ba su hana gudanar da tashe gaba daya a Jihar Kano ba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka kwana biyu bayan sanarwar da rundunar ta haramta gudanar da tashe a fadin jihar.

Kiyawa ya ce, “Ba hana tashe aka yi ba [gaba daya]; tashe irin wanda yara kanana suke yi da rana ko da safe a gidan iyayensu da makwabta, ba a hana wannan ba, haka kuma wanda ‘yan mata suke yi.”

Mai magana da yawun rundunar ya bayyana haka ne a hirarsa da shirin Najeriya A Yau, wanda Aminiya take gabartarwa a intanet.

Da yake wa shirin na Najeriya a yau bayani, Kiyawa ya ce tashen da ake gudanarwa da dare shi ne aka haramta a jihar, saboda bata-gari kan shigar rigar tashen su aikata miyagun laifuka.

“Tashen da ake yi da dare, wanda yawanci da ma ’yan daba ne suke fakewa da wadannan tashe, suna fitowa da makamai,” shi aka harmata, inji shi.

Ya shaida wa shirin na Aminiya cewa a lokacin irin wadannan tashe da ake gudanarwa da dare, ’yan daba, “Suna fitowa da makamai, za ka gan su daruruwa – da ma sun fito ne kawai domin fashin kayan mutane, sata da yin ta’adi.

“Ko motoci mutane suka samu a kan titi suna farfasawa; Wannan ne ya sa daga bayanan da aka samu aka dakatar da irin wannan nau’i na tashe,” kamar yadda ya bayyana.

A ranar Litinin, Aminiya ta kawo rahoto cewa Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta haramta yin tashe, wanda ake gudanarwa a bayan kwana 10 na farkon watan Ramadan, bisa hujjar bata gari, kamar masu kwacen waya kan fake da shi domin aikata barna a cikin al’umma.