✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu kai samame a CBN ba —DSS

Tun a bara dai labarin Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya soma yamutsa hazo.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta musanta rahotannin da ke cewa ta kai mamaya babban ofishin Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Abuja.

Tun a bara dai labarin Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya soma yamutsa hazo bayan da aka rika radin-radin cewa jami’an tsaron na sirri na nemansa ruwa a jallo.

Rahotanni sun bayyana cewa, tun bayan da ya ki amsa goron gayyatar Majalisar Wakilai dangane da wasu sabbin tsare-tsare da babban bankin ya kawo, CBN din ya bayar da sanarwar cewa Gwamnan ya yi balaguro zuwa ketare.

A wannan Litinin din ce dai Emefiele ya dawo Najeriya, inda bayan sa’o’i kadan rahotanni suka bayyana cewa jami’an DSS sun yi wa babban bankin dirar mikiya da sunan kama shi.

Sai dai DSS cikin wata sanarwar da ta fitar ta musanta zargin.

“Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta samu labarin karya da ake yadawa cewa jami’anta sun mamaye Babban Bankin Najeriya tare da kama gwamnansa, a yau 16/1/23. Wannan labari ne na karya kuma yaudara ce,” in ji sanarwar.

Tun ba yanzu ba dai wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta yi wa hukumar DSS shamaki da Gwamnan Babban Bankin Kasar.

Aminiya ta ruwaito cewa, Alkalin kotun, M.A. Hassan ne ya bayar da umarnin hana DSS din kama Emefiele.