✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu san yawan sabbin takardun kudin da aka buga ba —CBN

Babban Bankin Najeriya ya sanar cewa ba shi da masaniyar yawan sabbin takardun kudin da aka bugaba

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ba shi da masaniyar yawan sabbin takardun kudin da aka bugaba.

Mataimakiyar Gwamnan CBN Mai Kula Da Daidaiton Harkokin Kudi, Aisha Ahmad, ce ta sanar da haka a gaban Majalisar Wakilai, ranar Alhamis.

Aisha ta sanar da haka ne bayan Majalisar a gayyace ta domin amsa tambayoyi kan sabuwar dokar takaita cire tsabar kudi da bankin ya kaddamar.

Amsar tata ta zo ne bayan Dan Majalisa Sada Soli ya bukaci sanin adadin takardun sabbin kudin da CBN ya buga, yana mai nuna damuwa game da karancinsu, mako guda bayan an fara amfani da su.

Zaman kuwa na zuwa ne mako biyu bayan fara amfani da sabbin takardun kudi da CBN ya kaddamar, wadanda za su maye gurbin takardun N200, N500 da kuma N1,000 da ake amfani da su zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2023.

A ranar Laraba ne Majalisar ta yanke shawarar kirar Mataimakiyar Gwamnan CBN din, bayan ta samu wasika cewa Gwamnan Bankin, Godwin Emefiele, da ta gayyata ba zai samu halartar zaman ba saboda yana duba lafiyarsa a kasar Amurka.

Majalisar dai na son tattaunawa ne da bankin domin ganin ya sassauta dokar, wadda a farko ta takaita tsabar kudin da daidaikum mutane za su cira a mako zuwa Naira 100,000, kamfanoni kuma N500,000.

Sai dai a ranar Laraba da dare, sa’o’i kafin zaman CBN da Majalisar, bankin ya daga mizanin da ninkin biyar.

A halin yanzu, CBN ya kara yawan tsabar kudin da daidaikun mutane za su iya cirewa a mako zuwa N500,000, kamfanoni kuma Naira miliyan biyar.