✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu taba satar kudin gwamnati ba —Obi

Babu wanda aka taba samu yana zargi na da rashawa.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce shi da abokin takararsa Yusuf Datti sun tsarkaka daga duk wani zargi na cin hanci da rashawa.

Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya ce ko kadan ba a taba samunsu da satar kudin gwamnati ba, lamarin da ya sanya su kadai suka cancanci a kadawa kuri’a yayin Babban Zabe a watan gobe.

Furucin na Obi na zuwa ne a ranar Juma’a yayin taron yakin neman zabensa da ya wakana a filin wasanni na Rwang Pam da ke Jos, babban birnin Jihar Filato.

A cewar Obi, duk wasu masu jifansa babu abin da suke iya alakanta shi da shi face kiransa marowaci, “amma babu wanda aka taba samu ya zarge ni da rashawa.”

Ya ce a bisa wannan dalili ne jama’ar Najeriya za su sha kuriminsu muddin baitul malin kasar ya koma karkashin kulawarsa – saboda za a yi musu tattalinsa saboda amfanin al’umma ta yadda talaka zai dara.

Obi ya ce shi da abokin takararsa da sauran jiga-jigan jam’iyyar Labour, mutane ne masu karsashi da hazaka da kuzari sabanin ’yan takarar wasu jam’iyyun da ba sa iya wani kazar-kazar saboda tsufa.

Ya ce talauci, matsalar rashawa da kuma kalubalen tsaro duk za su zama tarihi a Najeriya muddin aka zabe shi.

A ranar 25 ga watan Fabrairu ne dai Hukumar Zabe ta Kasa INEC za ta gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Dokokin Tarayya a fadin kasar.