✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu tattauna batun Pantami a taron Majalisar Zartarwa ba – Lai Mohammed

Tuni dai muhawarar neman ganin Pantami ya sauka daga mukaminsa ta fara daukar salon bangaranci da banbancin addini.

Ministan Watsa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce babu wanda ya kawo batun Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami domin tattaunawa yayin taron Majalisar Zartarwa ta kasa ranar Laraba.

Pantami dai na fuskantar matsin lamba kan ya sauka daga mukaminsa a ’yan kwanakin nan kan zargin cewa yana goyon bayan kungiyoyin ta’addanci na Alka’ida da Taliban a shekarun baya.

Sai dai ministan ya musanta wadannan zarge-zargen, inda ya ce yana da kuruciya lokacin da ya yi wadannan kalaman kuma bai fahimci siyasar duniya sosai ba kamar yanzu.

Tuni dai muhawarar neman ganin Pantami ya sauka daga mukaminsa ta fara daukar salon bangaranci da banbancin addini.

Ministan dai ya sami halartar zaman na ranar Laraba wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A cewar minista Lai Mohammed lokacin da yake yi wa ’yan jarida jawabi a Fadar Shugaban Kasa, sam babu ma wanda ya taso da batun yayin taron.

Da aka tambaye shi ko majalisar ta tattauna batun da kuma yadda zai iya shafar kimar gwamnatin, sai ministan ya ce, “Bana son na yi magana kan batun shafar kimar gwamnati. Zan amsa tambayarka kai tsaye. Amsar ita ce ba mu tattauna ba,” inji shi.

Minista Pantami dai a daya daga cikin Tafsiransa na watan Ramadan a Masallacin Annur na Abuja ranar Asabar ya ce ya canza matsayinsa daga waccan fahimtar tasa ta baya.

Ya kuma yi zargin cewa akwai siyasa a irin tuhumar da ake yi masa.