✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu yarda a nada hadimar Buhari kwamishinar zabe ba —Sanatoci

Nadin ya saba doka don haka muna kira ga Shugaban Kasa ya janye shi, inji ’yan Majalisa

Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa, sun sun yi watsi da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na neman nada hadimarsa  Lauretta Onochi, a matsayin Kwamishina a Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

Shugaban Marasa Rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe, a wata gajeruwar sanarwa da ya aike wa wakilinmu, ya ce zabin Onochie a matsayinta na hadimar Shugaban Kasa Buhari ya saba wa kundin tsarin mulki.

Misis Onochie dai ita ce hadimar Shugaba Buhari ta musamman a kan shafukan sada zumunta.

Sanata Abaribe ya nemi Buhari ya janye bukatar da yake neman Majalisar ta amince da ita.

Abaribe ya ce, “da gayya a zabin Lauretta Onochie da Shugaba Buhari ya yi kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin wanda ya rantse zai kiyaye”.

“Sashe na ‘F’ sakin layi na 14 na kundin tsarin mulkin ya haramta wa duk wani dan jam’iyyar siyasa zama mamba na Hukumar INEC.

“Saboda haka mu ‘Yan Majalisar Dattawa Marasa Rinjaye ba mu yarda da wannan nadi ba kuma muna kira ga Shugaban kasa da ya janye shi.”

Shugaba Buhari a wasika da ya aike wa Majalisar, ya nemi ta amince da nadin Lauretta Onochie da wasu mutum uku a matsayin Kwamishinonin Hukumar Zabe ta Kasa.

A safiyar Talata ne Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya karanta wasikar mai dauke da jerin sunayen Kwamishinonin da ake neman Majasilar ta amince da su.

Sauran su ne Farfesa Mohammed Sani daga Jihar Katsina Katsina, Farfesa Kunle Ajayi daga Jihar Ekiti, sai kuma Sa’idu Ahmed daga Jihar Jigawa.