✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na bukatar yakin neman zabe a 2023 —Gwamnan Gombe

Gwamnan ya ce ba shi da bukatar yin yakin neman zabe duba da ayyukan da ya yi wa jihar.

Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce, babu bukatar ya yi yakin neman zabe a 2023, saboda gwamnatinsa ta yi ayyukan da ba a yi tsammani ba.

A cewarsa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, yana gogewar da ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba idan suka zabe shi a 2023.

“Muna bukatar ci gaba mai dorewa da karfafawa shi ya sa za mu zabi Tinubu, wanda ya ya yi alkawarin dorawa daga ayyukan alherin Buhari.

“Ina tabbatar muku cewa ba zai ba da kunya ba,” in ji shi, yana mai cewa Shugaba Buhari ya yi ayyuka masu tarin yawa na inganta rayuwar ’yan Najeriya.

Gwamnan Inuwa ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara Fadar Lamidon Gona, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, a yankin Amada a Karamar Hukumar da ke jihar.

Ya bukaci al’ummar masarautar da su zabi Jam’iyyar APC tun daga sama har kasa a zabe mai zuwa.

Ya jaddada cewa APC ce kadai Jam’iyyar da ta damu da halin da ’yan Najeriya ke ciki.