✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na takarar kowace kujerar siyasa – Shugaban ITF

Ya ce ba shi da aniyar tsayawa kowace irin takarar siyasa

Darakta Janar na Asusun horar da Masana’antu na Kasa (ITF), Joseph Ari, ya nesanta kansa da wasu fastocinsa da suka fara karade garin Jos, cewa zai tsaya takarar Sanata a zabe mai zuwa.

Shugaban ya alakanta hakan da yunkurin wadanda ya bayyana da masu kokarin bata masa suna.

Sir Joseph Ari ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar ’yan jarida da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato.

Ya ce mutanen suna nan suna manna hotunansa da na wasu ’yan takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa, cewa yana goyan bayansu.

Ya ce ya gano mutanen sun shirya za su je wajen da za a gudanar da babban taron zaben shugaban jam’’yyar na kasa, su manna wadannan hotuna da niyyar bata masa suna.

Ya ce, “Ina kira ga al’umma da su yi watsi da wadannan bata gari da suke kokarin bata mib suna. Kuma ina son na sanar da duniya cewa bana neman takarar kowace kujera, ta zaben siyasa.

“Ni na mayar da hankalina ne kan aikin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dora min na shugabancin Asusun ITF, don koya wa matasan Najeriya sana’o’i, domin su sami abin dogara da kansu,” inji shi.