✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da alaka da wata kungiyar ta’adda — Abdulsalami

Ana alakanta shi da jirgin da aka kama yana yi wa ’yan ta’adda dakon makamai da abinci.

Tsohon Shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya nesanta kansa tare da musanta alakanta shi da ake yi da ’yan daban daji da sauran kungiyoyin ta’adda da suka addabi al’umma a Jihar Neja.

Ya bayyana rahotanni da ke alakanta shi da ta’addanci a matsayin labaran karya marasa tushe ballantana makama.

Tsohon shugaban ya musanta zargin ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Dokta Yakubu Suleiman ya fitar a Minna, babban birnin Jihar Neja.

A cikin sanarwar, Abdulsamali ya yi zargin cewa akwai kafofin yada labarai na yanar gizo da ke alakanta shi da wani jirgi mai saukar Ungulu da aka kama yana yi wa ’yan daban daji dakon makamai da kayan abinci a wasu sassan jihar Neja.

A yayin da yake nesanta kansa daga wannan mummunan laifi da ya ce marasa kishin kasa na jingina masa, ya ce yana iya kawar da kai daga zargin amma ya ga bukatar fayyace gaskiya domin tarihi ya tuna da hakan.

“Irin wannan labaran na karya suna kara tabarbarewar matsalar tsaro da kasar ke fuskanta wanda bai kamata wani ya lamunta ba,” in ji shi.

Ya bayyana takaicinsa gami da damuwa kan yadda za a samu wasu su kago labaran bogi domin bata sunan wasu, inda yake kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da wannan mummunar dabi’a sannan su yi taka tsantsan da irin wannan bayanai na yaudara da ake yadawa a dandalan sada zumunta.

Kazalika, ya kuma bukaci ’yan najeriya da su ci gaba da dagewa wajen yi wa kasar addu’o’in samun zaman lafiya mai dorewa, yana mai cewa babu al’umma da za ta iya samun daukaka ba tare da zaman lafiya ta hanyar tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ba.