✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da burin da ya wuce yi wa ’yan Najeriya hidima —Atiku

A karon farko Atiku ya ziyarci Jihar Adamawa tun bayan lashe tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce ba shi da wani buri face yi wa ’yan Najeriya hidima.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin a garin Yola, babban birnin Jihar Adamawa a wani taro da dubban magoya bayan jam’iyyar APC suka sauya sheka zuwa PDP.

Atiku wanda gungun jama’a suka tarbe shi a dandalin Mahmud Ribadu da ke Yola, ya ce zai magance kalubalen da Najeriya ke fuskanta idan aka zabe shi.

Wannan dai shi ne karon farko da ya ziyarci mahaifarsa tun bayan lashe tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP.

Atiku ya bukaci al’ummar jihar da su hada kai da goyon bayan da suke ba shi tsawon shekara 30 da ya shafe yana siyasa.

Ya kuma yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar da su hada kai su yi aiki tare domin samun nasara a zaben na badi.

Ba zan sauka daga kujerata ba —Ayu

A halin da ake ciki, Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Dokta Iyorchia Ayu, ya ce ba zai sauka daga mulki ba duk da matsin lamba da ake yi masa na yin hakan.

Wasu rahotanni na cewa, Ayu na fuskantar matsin lambar sauka daga mukaminsa a wani bangare na sharuddan sasanta rikicin da ke tsakanin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.

Tun bayan kammala zaben fidda gwanin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar da kuma tsayar da gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin dan takarar mataimakin Shugaban Kasa, tsagin Atiku da na Wike suka takun saka.

Sai dai Ayu ya ce bai zai yi murabus ba, kuma ba shi da wani shirin yin hakan, yana mai cewa a shirye yake ya jagoranci jam’iyyar zuwa ga nasara a zaben 2023.