✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da hakurin da zan iya zama Sanata – El-Rufa’i

Ya ce sabanin sauran Gwamnoni, ba zai taba komawa Majalisa ba

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, ya ce ba shi da hakuri da juriyar da ake bukata ga ’yan majalisa shi ya sa ba zai tsaya takarar Sanata ba kamar sauran Gwamnoni masu barin gado.

Ya ce sabanin yadda takwarorinsa Gwamnoni masu barin gado ke rige-rigen zama Sanatoci, shi ba shi da hakurin aiwatar da ayyukan ’yan majalisa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron lakca kan ’yan majalisa karo na biyu da Cibiyar Ayyukan ’Yan Majalisa da Raya Dimokuradiyya (NILDS) a Abuja.

El-Rufa’i ya kuma ce, “Majalisa wani bangare ne na gwamnati da na tabbatar ba zan taba aiki a cikinsa ba. Yana bukatar naci da jajircewar neman goyon bayan mutane su goyi bayan kudurinka, wani abu da wasu daga cikinmu ba su da shi.

“Sabanin tafiyar da bangaren zartarwa wanda shi kai tsaye ne; da zarar an ce kai ne Gwamna ne, duk abin da ka fada ya zauna. Amma a majalisa, duk daya kuke, kuma babu abu mai wahala kamar sarrafa mutanen da kake kai daya da su.

“Sam ba na yi wa Shugabannin Majalisar Dokokin ta Tarayya kallon raini, saboda na san aikinsu kamar shi ne mafi wahala a Najeriya. Amma a bangaren zartarwa, za ka iya dauka ko ka yi kora. Na san akwai takwarorina Gwamnoni da za su koma Sanatoci, amma ina tabbatar muku cewa ni ba zan taba komawa ba,” inji shi.

Daga nan sai Gwamnan ya yaba wa Shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa mai ci da ke karkashin Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila, saboda yin muhimman dokokin da za su yi matukar tasiri ga ci gaban Najeriya.