✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da niyyar tsayawa takarar siyasa — Sanusi II

Sai dai ya ce zai ci gaba da wayar da kan al'umma a lokutan zabe.

Tsohon Sarkin Kano kuma Khalifan Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce ba shi da aniyar neman wani matsayi a siyasa.

Sai dai ya ce zai ci gaba da wayar da kan al’umma a lokutan zabe.

  1. Sojoji sun ceto daliban FGC Yauri 9 daga hannun masu garkuwa
  2. Babu wanda zai bar jami’a don bai biya kudin makaranta ba — Farfesa Sani Tanko

Sanusi ya yi wannan furuci ne a Kaduna ranar Alhamis, yayin wani zaman farko da ya yi da manyan Shehunnai da Mukaddamai na Darikar, tun bayan nada shi kalifanta na Najeriya.

A cewarsa, “Idan za mu samu wanda za su cika mana alkawuran da suka daukar mana, zamu yi aiki tare da su don ci gaban kasarmu, amma hakan ba siyasa ba ce.”

Ya ce rashin samun hakan na iya jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Ya kara da cewar, ya kamata a mayar da hankali kan ilimi musamman na kananan yara, wanda ta haka ne kawai a cewarsa za a iya warware wasu matsalolin kasar.

“Idan ba mu bawa yaranmu ilimi ba, yayin da wasu ke tura nasu yaran, daga karshe yaranmu za su zama ’yan aikinsu, shike nan ba abin da za mu iya,” inji Khalifa Sanusi.

A nasu bangaren, Shehunnan da suka kai masa ziyara sun ce duk da wannan shawara ta tsohon sarkin, Najeriya na bukatar addu’a.

Daya daga cikin malaman, Sheikh Halliru Maraya, ya tunatar da mutane kan bukatar su ji tsoron Allah a dukkan lamuransu, tare da kira ga shugabanni kan su kare rayuka da dukiyoyin wadanda suke mulka.