✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da shirin ficewa daga PDP – Gwamnan Abiya

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wani shirin gidan rediyo na musamman da aka yi da shi.

Gwamnan Jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ya musanta rade-radin da ke yawo cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.

Gwamnan ya musanta zargin ne a cikin wani shiri na musamman da ya yi da gidan rediyon jihar a ranar Asabar.

A cewar gwamnan, bai ga dalilin da zai sanya shi barin jam’iyyar PDP ba a halin yanzu.

Ya kara da cewa a wasu jihohin, da zarar gangar siyasa na kadawa sai ka ga ’yan siyasa sun shiga wasan sauya sheka.

Sai dai ya ce PDP a jihar Abiya, ta samar da dukkanin abin da mutanen jihar ke bukata, don haka batun sauya sheka bai ma taso ba.

Ya kuma ce har yanzu a Jihar l babu wanda ya gamsar da shi cewa akwai wata jam’iyya da ta fi PDP.

Ya ce a matsayinsa na shugaban gwamnonin PDP a Najeriya, ya gwammace ya zama ‘yaron mota da ya zama direba mara amfani’.