✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni na kori shugabannin kamfanin wutar lantarkin Abuja ba – Buhari

Fadar ta ce Buhari ba ya katsa-landan a harkokin kamfanoni masu zaman kansu.

Fadar Shugaban Kasa a ranar Laraba ta musanta cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin korar hukumar gudanarwar Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki na Abuja (AEDC).

Babban hadimin Shugaban kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, a cikin wata sanarwar ya ce zargin ba shi da tushe ballantana makama, kasancewar tun shekarar 2013 da gwamnati ta cefanar da harkokin lantarki, kamfanin ya koma hannun ’yan kasuwa.

Sanarwar ta ce sam ba Buhari ne ya umarci a kori shugabannin ba, kuma ba shi da hannu a ciki, don ba ya katsa-landan a harkokin kamfanoni masu zaman kansu.

“Fadar Shugaban Kasa na son yin tsokaci kan wani labari da ake alakantawa da Minista a Ma’aikatar Lantarki, cewa Buhari ya umarci a rushe tare da sake nada hukumar gudanarwar kamfanin AEDC.

“Wannan ba gaskiya ba ne. Tun da aka cefanar da harkar lantarki a 2013, kamfanin ya koma hannun ’yan kasuwa.

“Saboda haka babu hannunmu a ciki ko kadan a harkokin kamfani mai zaman kansa.

“Hatta Ministan da aka alakanta da sanarwar ya nesanta kansa da ita,” inji Fadar ta Shugaban Kasa.