✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ruwanmu da lallashin ’yan bindiga —El-Rufai

Ba zan biya ’yan bindiga kudin fansa ba domin aikina ne hukunta masu aikata laifi.

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce tattaunawa da ’yan bindiga ko lallashinsu ba ya cikin abin da jama’arsa suka zabe shi ya yi.

El-Rufai ya jaddada matsayin gwamnatinsa na rashin tattaunawa ko sulhu da ’yan bindiga, sai dai ya ce daidaikun mutane kamar malaman addini na iya yin haka a kashin kansu.

“Ba za mu tattauna da ’yan bindiga ko masu satar mutane ba, amma daidaiku mutane kamar limamai da malaman addini za su iya a kashin kansu, su yi musu wa’azi su tuba. Mu ma din muna so su tuba, amma ba aikinmu ba ne mu ce musu su tuba,’’ injis hi.

Ya yi jawabin ne bayan taron Majalisar Tsaron Jihar, kwana biyar bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 39 daga  Kwalejin Ganduna Daji ta Tarayya da ke Jihar, da suke neman kudin fansa Naira miliyan 500 a  kansu.

Ya kuma jaddada cewa gwamantinsa ba za ta biya ’yan bindiga kudin fansa ba domin aikinsa shi ne tabbatar da doka da kuma hukunta masu aikata laifi.

El-Rufai ya ce yawon kiwon shanu ya zama tsohon yayi saboda cigaban zamai da ya kai ga mamaye burtalin shanu.

Ya ce hanya mafi inganci ta magance matsalar rikicin manoma da makiyaya, satar dabbobi da ta’addancin ’yan bindiga shi ne makiyaya su rika zama a wuri daya domin su samu rayuwa mafi amfani ta yadda ingantaccen kiwon lafiya kuma ’ya’yansu za su samu ilimi.

A cewarsa, gwamnatin jihar na aiwatar da wani gagarumin shirin gandun kiwo da zai tsugunar da makiyaya 1,500 a Gandun Dajin Damau da ke Karamar Hukumar Kubau ta Jihar.

Ya bayyana cewa shirin zai ba wa makiyaya damar kiwata dabbobinsu a gandun kiwon da ke da ciyayi, makaranta, cibiyar lafiya lafiya; bugu da kari, ga abokan kasuwanci masu sayen nonon shanu.

Ya yaba wa jami’an tsaro bisa fadi-tashin da suke yi na tabbatar da ganin an samu aminci a Jihar, duk da matsalar tsaro da ke addabar ta.