✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ba sai dan wasa ya fadi a da’ira ta 18 za a ba da fenareti ba’

Ba sai dan wasa ya kai kasa a cikin da’ira ta 18 ba kafin a bayar da bugun fenareti.

Daga cikin sabbin tsare-tsaren da Hukumomin gasar Firimiyar Ingila suka kawo, a yanzu ba sai dan wasa ya fadi a da’ira ta 18 za a bayar da bugun fenareti ba. 

Hakan wani yunkuri ne karya kwarin gwiwar ’yan wasa daga kambama lamari idan aka rafke su ko an tade su a filin wasa wajen neman bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Haka kuma, Hukumomin sun kawo sabuwar dokar ta za ta rage yawan bayar da laifin satar fage mai janyo cece kuce, a shirye shiryensu na tunkarar kaka mai zuwa.

An shaida wa alkalan wasa a gasar cewa su rika la’akari da karfin dukan da dan wasan baya ya kai, tasirinsa da kuma niyyarsa kafin su yanke hukunci.

Bisa la’akari da wannan sabuwar doka, a yanzu ba sai dan wasa ya kai kasa a cikin da’ira ta 18 ba kafin a bayar da bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Daga cikin sabbin tsare-tsaren da aka tanada domin tunkarar sabuwar kaka mai zuwa, a yanzu alkalan wasa za su daina dakatar da wasa saboda laifukan da ba su taka kara sun karya ba.

Shugaban alkalan wasa na gasar Firimiyar Ingila, Mike Riley ya ce makasudin wannan sauye sauye shine a kashe tsaiko a wasan kwallon kafa.

Haka kuma sabuwar dokar satar fagen zai rage yawan tsaiko da ake samu sakamkon amfani da na’urar VAR.