✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa nake sana’ar tukin Keke Napep —Amina “Sai Mama”

Mai ’ya’ya bakwai, Sai Mama ta ce tana matukar alfahari da sana’ar duk da cewa maza ne suka fi shahara a cikinta.

Tukin Keke NAPEP ko “A Daidata Sahu”, kamar yadda ake kiran shi a Kano, sana’a ce da aka san maza da ita.

Amma wakiliyar Aminiya ta yi kicibis da wata baiwar Allah mai ’ya’ya bakwai mai wannan sana’a, har ma matar mai suna Amina Ibrahim – wadda ake yi wa lakabi da “Sai Mama” – ta rage mata hanya.