✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za a bar ’yan sama da shekara 65 su je Aikin Hajjin bana ba

Hukumar ta ce umarnin ya fito ne daga kasar Saudiyya

Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar Katsina ta ce ba za a bar maniyyata ’yan sama da shekara 65 su je kasar Saudiyya don sauke farali a Aikin Hajjin bana.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, Alhaji Badaru Bello-Karofi ya fitar a Katsina.

Hukumar, a cewar sanarwar, ta bayyana hakan ne yayin da take taron wayar da kan jama’a a kan shirye-shiryen Aikin Hajjin bana.

A dai shirya taron ne a cibiyoyin ba da horon da ke Kananan Hukumomin Kankiya da Dutsinma, da nufin wayar da kan jama’a.

Sanarwar ta ce, “Saudiyya ta nuna cewa kada a bar ’yan sama da shekara 65 su je Aikin Hajjin bana, sannan ta tunatar da maniyyatan cewa yin rigakafin COVID-19 dole ne.

“Dole ne a yi wa kowa dukkan zagaye uku na cutar,” inji Shugaban hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu-Kuki.

Tun da farko dai Shugaban ya yaba da yadda aka gudanar da taron, tare da kiran maniyyatan su tsarkake niyyarsu kafin lokacin aikin.

Ya ce Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanya Naira miliyan 2.5 a matsayin kafin alkalami na kudin kujerar bana.