✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Ba za a yi zabe a mazabu 240 ba – INEC

INEC ta ce mazabun na cikin jihohi 28 da Abuja

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ba za a yi zaben 2023 ba a mazabu 240 da ke sassan kasar nan daban-daban.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taro da jam’iyyun siyasa ranar Litinin a Abuja.

Farfesa Yakubu ya ce mazabun na warwatse ne a cikin jihohi 28 da ma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Ya ce nan ba da jimawa ba hukumar za ta fitar da cikakken sunayen rumfunan da lambobinsu da mazabu da Kananan Hukumomin da suke da kuma Jihohinsu.

Shugaban ya kuma ce INEC ta tattara cikakken kundin rajistar, inda ya ce ofisoshinsu na Jihohi za su sanar da wuraren yadda ya kamata, musamman ga mutanen da ba su bayar da lambobin wayarsu ba yayin rajistar, ko kuma sun canza wasu.

Ya ce, “Mazabun guda 240 din na cikin Jihohi 28 da yankin Abuja ne babu wadanda suka yi rajista a cikinsu. Akwai Jihohin da suke da mazaba daya, akwai masu har guda 12 kuma, in ban da Taraba da Imo da ke da mazabu 34 da kuma 38 kowacce.

“Babu sabbin masu zabe da suka zabi mazabun, sannan babu wadanda suka bukaci a canza musu wuraren zabe zuwa wadancan akwatinan yayin rajistar da aka kammala a bara, galibi saboda dalilan tsaro. Hakan na nufin ba za a yi zabe a cikinsu ba.

“Hakan na nufin yanzu yawan mazabun da za a yi zabe ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris sune guda 176,606. Akwai cikakken sunayen mazabun a cikin takardun da muka ba ku na wannan taron.

“Baya ga haka, ’yan Najeriya na da damar sani wadannan wuraren, kuma nan ba da jimawa ba za mu dora cikakkun sunayensu a shafinmu na intanet da shafukan sada zumunta saboda jama’a su sani.”

Sai dai Shugaban na INEC ya bukaci masu zabe da su tabbatar da mazabunsu ta shafin hukumar na intanet, yana mai cewa dukkan masu zaben da aka canza wa rumfuna za ai aike musu da sako a kan hakan ta wayoyinsu.