✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu dage zaben 2023 ba – INEC

INEC ta ce ta yi wa zaben 2023 kyakkyawan shiri.

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce hukumar ba ta tababa kan jadawalin babban zaben 2023 da ta tsara balle kuma ta dage shi.

Yakubu ya bayyana haka ne ranar Laraba a Abuja sa’ilin da yake mika wa shugabannin jami’yyu kwafin sunayen masu zaben da aka yi wa rajista su 93,469,008.

Ya ce fiye da kowane lokaci, INEC ta yi kyakkyawan shiri don gudanar da zaben 2023.

Ya kara da cewa, kawo yanzu, hukumar ta samu nasarar aiwatar da ayyuka 11 daga cikin 14 da ta shirya aiwatarwa dangane da zaben na 2023.

“An riga an tura wasu muhimman kayayyakin aiki zuwa sassa daban-daban na kasar.

“An karbi kashin karshe na na’urar tantance masu zabe (BVAS), kuma nan ba da dadewa ba za a kammala aikin saita su.

“Mun fara jigilar wasu muhimman kayayyakin aiki zuwa jihohin kasar a cikin kwanaki biyun da suka gabata.

“Jihohi 17 a shiyyoyin siyasa uku sun riga sun karbi kayayyakinsu.

“Bugu da kari, an buga Katin Zabe guda 13,868,441 an kuma mika su ga jihohi don raba wa jama’a bayan rajistar da aka yi wa sabbi ko wadanda suka sauya wurin zama kamar yadda doka ta tanadar,” in ji Yakubu.

A cewarsa, hukumar ta sake tattara sabon kundin sunayen wadanda aka yi wa aijista bayan gyare-gyaren da ta yi a na farkon da ta baje wa ‘yan kasa.