✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu dauki Ronaldo ba a bazarar nan —City

Makomar Cristiano Ronaldo a fagen kwallo na ci gaba da kasancewa cikin yanayi na rashin tabbas, bayan da zakarun gasar Firimiyar Ingila, Manchester City, suka…

Makomar Cristiano Ronaldo a fagen kwallo na ci gaba da kasancewa cikin yanayi na rashin tabbas, bayan da zakarun gasar Firimiyar Ingila, Manchester City, suka yi watsi da tayin kulla yarjejeniya da shi daga Juventus a bazarar nan.

Duk da yake tsohon tauraron na Real Madrid ya musanta tuntubar City cikin wani sako da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a makon da ya gabata.

Sai dai wasu rahotanni daga kafafe da dama a Turai sun nanata cewa yanzu haka Ronaldo yana matsa lamba don rabuwa da Juventus kafin rufe kasuwar hada-hadar sauyin shekar ‘yan wasa a wannan bazara.

Fitacciyar Jaridar wasanni ta L’Equipe da ke Faransa, ta ruwaito cewa a halin da ake ciki, wakilin Ronaldo, Jorge Mendes, yana birnin Manchester kasancewar yana wakiltar dan wasan City, Bernardo Silva, wanda ke neman barin kungiyar a bazarar nan.

A cewar jaridar L’Equipe, Mendes yana kokarin kulla yarjejeniyar musaya da za ta kai ga Silva ya koma Juventus, Ronaldo kuma ya koma City.

Sai dai ga dukkanin alamu City ba ta son sanya Ronaldo zama daya daga cikin masu samun albashi mai tsoka a kungiyar ganin yawan albashin sa a Juventus.