✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu goyi bayan juyin mulki ba – Afenifere

Afenifere ta ce halin da kasar ke ciki ne ya harzuka wasu suka fara kiraye-kirayen sojoji su yi juyin mulkin.

Kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere ta ce ba za ta goyi bayan kowanne irin yunkurin juyin mulki ba.

Kungiyar, a cikin wata sanarwa ranar Juma’a ta ce halin da kasar ke ciki ne ya harzuka wasu suka fara kiraye-kirayen sojoji su yi juyin mulkin.

Kakakin kungiyar, Kwamared Jare Ajayi a cikin sanarwar ya ce juyin mulki ba shi da kowanne irin amfani kuma zai mayar da kasar baya ne in har aka yi shi.

Jare ya ce, “La’akari da halin da muka shiga zamanin mulkin sojoji, ba za mu taba goyon bayan kowanne irin yunkuri na komawa gidan jiya ba.

“Muna sane da yadda ake take hakkokin mutane da haramta kungiyoyin fararen hula da kuma karkashe ’yan kishin kasa saboda kawai sun nuna adawa da mulkin sojojin.

“Idan ma aka yi duba na tsanaki za mu iya cewa illar mulkin soja ta fi ta amfaninsa a Najeriya. Duk da yake ba ma goyon bayan juyin mulkin, amma ba zai hana mu ci gaba da fafutukar ganin al’amura sun inganta ba.

“Abin takaici ne matuka yadda ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka koma yanzu sune masu juya akalar gwamnati a Najeriya, wai har mamaye wasu sassa na kasar suke yi. Abubuwa ba su taba lalacewa irin haka ba,” inji Afenifere.

Kungiyar ta ce matukar gwamnati ta gaza wajen kare ’yan kasarta, to ba shakka dole su fara neman kowacce irin mafita da kansu.

Daga nan sai kungiyar ta yi kira ga gwamnati ta kara tashi tsaye wajen kawo karshen ayyukan ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ’yan bindiga ta hanyar kawo karshen wariya da kuma mututnta kowa.