✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu hana amfani da shafukan sada zumunta ba a Afghanistan – Taliban

Sai dai kungiyar ta ce ba za ta lamunci yada labaran karya ba.

Kungiyar Taliban a Afghanistan ta musanta cewa tana da shirin hana amfani da shafukan sada zumunta na zamani.

Kakakin kungiyar, Suhail Shaheen ne ya bayyana hakan ranar Talata.

Ya ce Taliban ta yi amanna da ’yancin fadin albarkacin baki, inda ya ce a shirye suke su karbi suka mai ma’ana daga kowanne sashe.

Sai dai ya ce ba za su lamunci yada labaran karya ba.

Ya ce, “Sam ba mu da shirin saka kowanne irin takunkumi a kan amfani da shafukan sada zumunta. Mun yarda da ’yancin fadin albarkacin baki.

“Idan wani ya soki salon mulkinmu, ko ya bayyana wani ra’ayi ko da kuwa ya saba da namu, za mu dauke shi a matsayin ’yancin fadin albarkacin baki.

“Amma babu shakka ba zamu bari a rika kirkirar labaran kanzon kurege ba, ba za mu lamunci wannan ba. Amma duk abin da ba wannan ba, ba mu da matsala da kowa,” inji Suhail. (NAN)