✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu iya ci gaba da sayar da fetur a kan N165 ba – IPMAN

IPMAN ta ce ba za ta iya sayar da man a kasa da N180 ba

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta ce sakamakon rashin kyawun yanayin kasuwanci, mambobinta ba za su iya ci gaba da sayar da man a kan N165 kan kowacce lita ba.

Shugaban kungiyar reshen Jihar Legas, Akin Akinrinade, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Litinin, inda ya ce babu dan kasuwar da ke harkar man da zai siyar da shi kasa da Naira 180.

Kazalika, ya ce sakamakon haka sa za su rufe tashoshin sauke man, ba wai don suna yajin aiki ba.

Ya ce, “Ka ga idan za ka yi lodin man, kowacce lita sai ka biya mata naira 165, ga kudin sufurinsa kan Naira 6 muke yi, wani lokacin ma Naira 8, ya dai danganta da nisan gurin daga Legas, idan wajen Legas ne ma ya fi haka.

“To idan ka kara Naira takwas kan 162, ya zama 170 kenan. Kuma gwamnati ce ke tsara rarraba man nan, ga shi tana so mu sayar kan Naira 165, a haka ma ba mu kara da kudin sauke man ba, da na dawainiya da shi a tashoshinmu,” inji Shugaban.

Shugaban na IPMAN ya kuma ce tashin farashin man Dizal da na wutar lantarki na cikin abubuwan da za su haddasa kara kudin fetir din.

“Muna amfani da janareta mai amfani da dizal, kuma yanzu 800 ne lita daya, kin ga babu wata tashar sauke man fetir a Legas da take amfani da kasa da lita 50 a rana,” inji shi.

Dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai dai ya fara zamowa tamkar ruwan dare a baya-bayan nan a jihohi da dama na kasar nan, baya ga rashin tsayayyen farashi da yake da shi a yanzu, sakamakon karin da gidajen mai suka yi masa da farashi daban-daban.