✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu taba bari Najeriya ta ruguje ba – Buhari

Buhari ya ba wa 'yan Najeriya tabbacin cewa babu wani abu da zai bari ya raba ta a matsayin kasa daya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai bari kowanne irin tashin hankali ya zama sanadin rugujewar Najeriya ba.

Ya ce ya kamata duk ‘yan Najeriya su yi watsi da tashe-tashen hankulan da ka iya kawo rabuwar Najeriya a matsayin kasa daya.

Buhari wanda ya sami wakilcin Babban Sakatare a Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya bayyana hakan ne a wajen bikin ranar Gidauniya da Tattaunawa na Jami’ar Ibadan, wanda aka gudanar a Cibiyar Taron Kasa da Kasa da ke Ibadan ranar Talata.

A cewar Buhari, “Bari na kara jadadda mana cewa rabuwar kan ‘yan Najeriya ba abin da za a tattauna ba ne.

“Saboda haka ya kamata a yi kokarin kare ta a matsayin dunkulalliyar kasa.

“Danhaka ya kamata a yi watsi da duk wasu tashe-tashen hankula da rikice-rikice.

“A cikin yanayin zaman lafiya ne kadai za mu iya cimma abubuwan ci gaba da muka sa gaba. ”

Dangane da yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke yi kuwa, shugaban ya ce ya amince da ‘yancin ma’aikata na bayyana korafinsu, ya ce akwai ramuwar gayya tsakanin ma’aikatan da kungiyoyin kwadago.

Buhari ya kara da cewa kafa Kwamiti domin bibiyar yadda ake zaben shugabannin jami’o’in kasar na daga cikin matakan da aka dauka, biyo bayan korafe-korafen da aka gabatar gaban Gwamnatin Tarayya dangane da badakalar cin hanci da rashawa da ke faruwa a wasu jami’o’in kasar nan.