✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba za mu yarda a yi sulhu a fitar da dan takarar APC ba — Magoya bayan Tinubu

Sun ce kamata ya yi a saka wa gudunmawar da Tinubu ya ba Buhari a 2015

Kungiyoyin magoya bayan mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, sun yi fatali da yunkurin yin sulhu wajen fitar da dan takarar jam’iyyar.

Kungiyoyin, wadanda ke karkashin NYPT da TSO, sun ce ya kamata a saka wa tsohon Gwamnan na Jihar Legas saboda irin rawar da ya taka wajen yin nasarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a 2015.

Da suke karanta matsayin kungiyoyin a wani taron manema labarai a Abuja, Ko’odinetocin kungiyoyin, Abdullahi Tanko Yakasai da Aminu Suleiman, Yakasai, sun roki Shugabancin jam’iyyar karkashin Sanata Abdullahi Adamu da ya bari a fafata a zaben.

A cewar Abdullahi Yakasai, muddin APC na son ta ci gaba da rike mulki a 2023, ya zama wajibi ta gudanar da sahihin zaben dan takararta.

Ya kuma yi kira ga daliget din jam’iyyar da kada su yarda su karbi kudi daga ’yan takara don sayar da kuri’unsu.

“Bai kamata a ce a wannan lokacin APC ta kyale san zuciyar wasu tsiraru ya hana yin adalci da bin dokokin Kundin Tsarin Mulki wajen yin zabe ba.

“Mu na ganin hakan a matsayin wani yunkurin da wasu makiya na cikin jam’iyyar ke kokarin yi wajen tadiye jagoranmu, Bola Tinubu.

“Jiya [Talata], Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayin jawabinsa ya bayyana karara cewa muna bukatar jajirtaccen dan takara da zai kai jam’iyyar ga tudun mun tsira,” inji shi.