✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu yafe wa Aisha Yesufu ba —Zahraddeen Sani

Jarumin ya yi zargin akwai boyayyiyar manufa a zanga-zangar #EndSARS

Zahraddeen Sani, daya daga cikin fitattun jaruman masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, ya ce mutanen Arewa ba za su yafe wa Aisha Yesufu ba, saboda jagorantar matasa wajen shirya zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali.

Jarumin ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Zahraddeen ya ce “ba za mu taba yafe miki ba, saboda mun san cewa ke ba ‘yar asalin Arewa ba ce, an yi amfani da ke wajen ta da hankali.

“Kin tunzura bata-gari sun shiga zanga-zanga wanda daga karshe suka koma fasa shagunan mutane.

“A Kano sun fasa shagon Galaxy Mall da ke Sabon Gari”, a cewar jarumin.

Jarumin ya kalubalanci Aisha Yesufu cikin bidiyon da ya shafe tsawon minti hudu yana magana, ya yi zargin cewa tun farko an shirya zanga-zangar ne na da wata boyayyiyar manufa.

Tun farkon zanga-zangar #EndSARS wasu daga cikin jaruman Kannywood sun ki aminta su shiga, saboda zargin an shirya hakan ne domin kawo wa Gwamnatin Shugaba Buhari tarnaki.