✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan halarci taron tattaunawa da ‘yan takarar Shugaban Kasa ba —Kwankwaso

An shirya taron ne da wata manufa ta daban.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai halarci taron tattaunawa da ‘yan takarar Shugaban Kasa ba da za a yi a gobe Litinin.

Bayanai dai sun tabbatar cewa hadakar wasu kungiyoyin Arewacin kasar ne suka shirya taron domin kowane dan takara ya gabatar da manufofinsa na zama shugabantar kasar.

Hadakar kungiyoyin Arewacin kasar da suka shirya taron sun hadar da Kungiyar Arewa Consultative Forum, da Kungiyar Arewa House, da Gidauniyar Sir Ahmadu Bello, da Kungiyar Dattawan Arewa da kuma Kungiyar Bincike da Ci gaban Arewa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Kwamitin Yakin Neman Zaben Kwankwaso, Abdulmumin Jibrin, ya wallafa a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa Kwankwaso ya riga ya shirya yakin neman zabe a ranar da aka tsara zai yi jawabi a taron.

Sannan kuma sanarwar ta yi zargin cewa sun sami sahihin labarin da ke cewa wasu daga cikin masu shirya tattaunawar na da wata manufa, sannan kuma za su yi amfani da taron ne wajen nuna goyon baya ga wani dan takara.

An dai tsara cewa Kwankwaso zai yi jawabi a gaban taron tattaunawar ranar Litinin, tare da dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Asabar ce dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP,  Atiku Abubakar ya gabatar da nasa jawabin.